WAEC ta saki kashi 80 na sakamakon jarrabawar 2021

Daga BASHIR ISAH

Hukumar shirya jarrabawa ta WAEC ta saki sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na 2021.

Shugaban WAEC a Nijeriya, Patrick Areghan, shi ne ya bayyana sakin sakamakon a ranar Litinin.

Areghan ya ce adadin ɗalibai 1,573,849 ne suka yi rajistar WASSCE a tsakanin makarantu 19,425 da hukumar ta amince da musu, yayin da ɗalibai 1,560,261 ne suka rubuta jarrabawar.

A cewarsa, ɗalibai 1,274,784 ne suka samu makin ‘Credit’ zuwa sama da haka a tsakanin darussa biyar haɗa da darasin Ingilishi da na lissafi, sannan ɗalibai 1,560,261 sun samu ƙasa da haka.

Ya ƙara da cewa, an riƙe sakamakon ɗalibai 170,146 bisa dalilin maguɗin jarrabawa.

Ya ci gaba da cewa, WAEC ta riga ta tantance tare da sake sakamakon ɗalibai 1,256,990 wanda shi ne kwatankwacin kashi 80.56% na adadin ɗaliban da suka rubuta jarrabawar a faɗin Nijeriya.

Areghan ya ce har yanzu suna kan tantance sakamako guda 303,271 kwatankwacin kashi 19.44% na jimillar ɗaliban da suka rubuta jarrabawar.

Jami’in ya bayyana cewa, jinkirin da aka fuskanta hakan ya faru ne sakamkon wasu ɗaliban da ‘yan matsaloli dangane da darussansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *