Wuce iyaka a kan kishi

Daga AMINA YUSUF ALI

Assalamu alaikum. Masu karatu sannunku da jimirin karanta wannan fili namu na Zamantakewa Wanda yake zuwar muku kowanne mako a jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan makon za mu tattauna a kan zafin kishin mata da abinda yake kawo shi, da kuma yadda za a magance shi. A sha karatu lafiya.

Kafin na shiga rubutun gadan-gadan. Ya kamata na tuna wa ‘yanuwana mata cewa: mu ne jinsin da muka fi nuna muna da haɗin kai yayin da wata ‘yaruwarmu ta shiga wani hali fiye da maza. Kuma mu ne kullum muke iƙirarin cewa ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne. Wato duk abinda ya samu mace ɗaya, to ya shafi dukkan mata. Amma abinda zai ba da mamaki. Daga maganar namiji ta gifta tsakaninki da ‘yar’uwarki, sai kuma zancen ya sauya. Ya zama kuma macen ce take jefa ‘yaruwarta a lalurar. Maimakon ta zama mai magance mata. Wato dai mai dokar bacci ya ɓige da gyangyaɗi. Duk da dai wasu lokutan a kan samu matan da suke riƙe ‘yanuwansu cikin amana.

Misalin irin wannan shi ne; yadda kishiya take zaluntar kishiyarta saboda sun ha]a miji. Kuma kowacce ba ta da burin a ce ɗayar aurenta ya mutu ta fice ta bar mata gidan. Ko mu dubi yadda uwar miji kan gallaza wa surukarta ko yadda suruka take gallaza wa Uwar miji. Ko kuma yadda dangin miji mata suke gallaza wa matar ɗanuwansu. Idan kuma damar a hannunta take ta gallaza musu. Ko kuma mu dubi yadda matar Uba kan zalunci ‘ya’yan miji da makamantansu. Abun dai ba sauƙi ko ta wanne ɓangare. Amma abin tambayar me ya sa sai mu mata, mata, mata!

Ba don kada ma a ce na matsa da yawa ba, sai na ce; ko ƙannen miji maza da suke gallaza wa matar wansu. Yawanci idan ka bincika za ka ga akwai zugar mace a ciki. Amma abin mamakin sai ka ga mun fi kowa ihu da tutiyar mace ta mace ce. Bayan kuma idan muka nutsu za mu ga dukkan ciwon da ya addabi mace, wata macen ce sila. Ko neman mata da maza suke yi suke cutar da matansu da wa suke yi? Da wata macen suke yi ‘yaruwarta. To ina mafita? Anya kuwa ciwon ‘ya macen na ‘ya macen ne?

‘Yaruwa ki sani, kafin ki zama kishiya, ko dangin miji ko matar Uba, da sauransu. Sai da kika fara zama musulma. To kamaata ya yi ki fara sa haƙƙin ‘yanuwartakar musulunci fiye da komai a mu’amalarku. Ba a ce dai ki zauna a cuce ki, ko a tauye miki haƙƙinki ba. Amma ki nemi haƙƙinki ba tare da kin cutar da kowa ba.

Da farko dai zan fara da Uwargida. Ba don komai ba don ita ce ta fari kuma Hausawa sun ce daga na gaba ake ganin zurfin ruwa. Kuma kishi ya fi zafi daga uwargida. Domin kusan dukkan labaran idan ma ba dukkansu ba. Da suke ta yawo na zafin kishi yawanci iyayen gida su suka fi wuce gona da iri. Iyayen gida su ne kan gaba wajen ɗaukar ran kishiyoyinsu ko na mazajensu yayin da suka yi yunƙurin yi musu kishiya. Wannan yana faruwa ba don komai ba sai don rashin son wata macen ta shigo gidanta ta yi tarayya da ita a kan mijinta da kuma dukiyarsa, kada a da]a kada a rage. To kun ga wannan ya saɓa da koyarwar musulunci da kuma halin nagarta.

Kishi na musulunci wanda matan Annabi S.A.W suka yi, shi ne na yin rigegeniya wajen kyautata wa miji. Ba wai ƙoƙarin sai an cutar da kishiya ko an fitar da ita ba. ‘yanuwa ku sani, baƙin kishin nan zai iya jawo miki asarar Lahirarki. Kishiya ba daga kanki aka fara ba, ɗagawar ta mece ce?

Ya ke Uwargida ki sani: kasancewarki ta farko a wajensa ba wayonki ba ne ko dabararki ba ce, ko zaɓinki ba. Allah ne ya ƙadarta cewa ke za ki fara zama matarsa. Kuma ki sani a kan jarrabawa kike. Allah jarraba ki yake don ya ga gudun ruwanki. Kuma ki sani, wannan matsayin naki na Uwargida idan kika yi zalunci zai iya kai ki ga halaka ta Duniya da Lahira. Haka ki sani, shi auren da mijinki ya ƙaro ba wai cin amanarki ya yi ba. Haƙƙinsa ne da Allah Ya ba shi na ya ƙaro mace daga ɗaya zuwa huɗu, idan har zai yi adalci. Saboda haka ɗagawa da ji da kai ba naki ba ne.

Da ke da wacce aka auro duk haƙƙinku ɗaya a wajen mijinku. Haka Allah ya shar’anta. Al’ada ce kawai ta mayar da ke Uwargida. Idan kika yi wasa da haƙƙin Allah kuma kika sa girman kai kika bijirewa Allah, Shi ma zai iya nuna miki mulkinsa a kanki kuma ya zare albarka da walwala a rayuwarki. Shi kansa mijin da kike taƙama, A zare albarkar dake dukiyarsa. Don haka ki daure zuciyarki ki yi komai cikin tsoron Allah. Ke ma ba ki san naki yaran ina za su je ba. Ki sani ita ma Amaryar ba son ranta ne ta aure miki miji ba. Ita ma da so samu ne, za ta samu kamar taki, da ta fi son ta auri mijinta ta zauna daga ita sai shi. Amma ita ma wata jarrabawa ce a kanta da aka ƙadarta ta auri naki mijin.

Ke kuma Amarya ki sani, ba ƙasƙanci ba ne don Allah ya ƙadarto miki kasancewa matarsa ta biyu. Wannan yana cikin rubutacciyar ƙaddararki. Ki zauna da amana da kishiyarki da yaranta. Ki sani maza suna ƙara aure ne saboda sun samu ƙarin wadata, ko suna buƙatar ƙaro auren, ko ma wasu dalilan. Ki cire a ranki cewa zai aure ki saboda bai son matarsa ko ta gundure shi. Idan yana da yara ki so su. Wannan shi ne zai nuna kina son ubansu da gaske. Idan ma mutuwa Uwargidan ta yi ko fita ta yi. Ki ri}e mata ‘ya’ya cikin adalci. Sai ke ma Allah ya duba naki. Don ba ki san yadda rayuwa za ta yi da ke ba.

Amma fa sai kin toshe kunnuwanki. Domin ita Amarya dankali ce sha kushe. Al’ummarmu ta Hausawa kullum ana ganinta a matsayin muguwa ko mai rusa farin ciki wacce ta shiga tsakanin masoya guda biyu. Kuma ba wai a wajen kishiyarta kawai ba. Har ma a wajen sauran matan gari. Ba macen da take yi wa Amarya uzuri sai wacce ‘yarta ko ƙanwarta ko wata ‘yaruwarta za ta yi aure ko ta yi aure ta je a matsayin ta biyu. Kuma ƙaddara ce da za ta iya faruwa kan kowacce mace.

Amarya ki sani, idan kika samu fada a wajen miji kada ki zalunci kishiyarki ko yaranta. Ke ma idan Allah ya ba ki ‘ya mace ba za ki so kishiya ta azabtar da ita ko yaranta yadda kika azabtar da wata ko ‘ya’yanta ba. Haka ku dinga kula da haƙƙin dangin miji, musamman mahaifi da mahaifiyarsa. Domin watarana ku ma iyayen miji ne. Ba za ku so a gallaza muku yadda kuka gallaza wa surukanku ba.

Hakazalika, akwai kuma dangin miji da suke ƙoƙarin dole sai sun kawo ruɗu da rashin zaman lafiya a cikin gidan ɗanuwansu. In dai ɗan’uwansu ya zauna lafiya da matarsa, to sai a shiga zargin ta magance shi ne. Ba biyayyarta ko halayen kirkinta ya sa yake sonta ba. Babban abin takaicin shi ne, ƙannen miji musamman ma mata su ne suke fara assasa matsalar. Uwar miji in dai dattijuwar arziki ce mai addini ba za ta bi wannan yariman ta sha kiɗa ba. Amma abin takaici, ita ma sai ta zama ‘yar amshin shatan ‘ya’yanta.

Haka idan mijin na da ƙanne ko yayye maza, idan masu biye mata ne, nan ma a sake samun masu bin ayarin muzguna wa matar yayansu. Wani lokacin ma har da kishin sauri. Wato kishin da ake yi tsakanin matar wa da ƙani (faccaloli). Shi kuma wannan ma ya fi kowanne muni. Don zai iya sanadiyyar da za ta sa ‘yanuwan jini su zama abokanen gabar juna. Saboda kawai matansu ba sa jituwa. Kuma kowa yana goyon bayan tasa. Waɗannan misalai suna da yawa idan na ce zan ta lissafowa, filin nan ma ba zai isa a gama lissafo su ba.

Kada mai karatu ya manta fa duk waɗannan halaye da na lissafo a sama, mata sukan tsinci kansu suna aikata su ne kawai idan namiji ya gifta a cikin alaƙarsu da mace ‘yaruwarta. Kuma kishi shi yake haddasa hakan. Kowacce daga cikin matan tana neman samun matsayi ma fi girma daga wajen namijin. Kuma tana ganin haƙanta ba zai cim ma ruwa ba har sai ta dusashe tauraruwar wata. Wanda hakan son zuciya ne mai girma. Haka a musulunce, a al’adance ko a mu’amalance bai dace ba.

Daga ƙarshe ina kira ga ‘yanuwa mata da su zama masu tausayawa da adalci ga yanuwansu na jinsi. Ki sani, idan kika zama sanadiyyar ƙuntata wa rayuwar wani ko wata, to ke ma ko ba daɗe, ko ba jima; za ki girbi abinda kika shuka. Zan dakata a nan. Ina jinjina ga masu kira su ba da shawara ko tsokaci. Haƙiƙa kuna raina har kullum kuna ƙarfafata. Na gode.