Wane irin faɗi hukumar ƙididdiga NBS za ta yi wa tattalin arziki?

Spread the love

Labaru sun yaɗu musamman a shafukan jaridu da kuma kafafen yanar gizo kan shirin Hukumar ƙididdigar Tattalin Arziki ta Nijeriya ‘NATIONAL BUREAU OF STATISTICS’ (NBS) na wani shirin faɗaɗa hanyoyin ƙididdigar mizanin ƙarfin tattalin arzikn ƙasa GDP da sanya wasu abubuwan da a baya ba ta taba shigar da su ba. Gaskiyar magana abubuwan sun haddasa muhawara don tunanin ko ma dai su na da wata gudunmawa ga tattalin arzikin to ai ba hanyoyi ne da kasa ta amince da su a hukumance ba. Idan a ka ƙara abubuwan zai yiwu mizanin tattalin arzikin na Nijeriya ya nuna ƙasar ta na gaba da ƙasashe kamar yadda ya taɓa faruwa a shekarun baya inda a 2014 a ka gudanar da bitar mizanin na GDP da ya sanya Nijeriya ta zama ta kan gaba a tattalin arziki a nahiyar Afurka fiye da Afurka ta kudu mai manyan masana’antu. Ba za a yi babban mamaki ba don duba hada-hadar kuɗi a Nijeriya da ta haɗa hatta da wasu manyan kamfanonin Afurka ta kudu ga kuma mallakar yawan jama’a inda Nijeriya ke da mafi yawan jama’a a Afurka da kuma zama mafi yawan ƙasar baƙar fata a duniya. A lokacin akwai abubuwan da a ke lissafin mizanin da su da ba su wuce guda 740. Yadda za a kara fahimtar bayanin shi ne an yi la’akari da kayan da a ke saye da sayarwa da buƙatar jama’a kan hidima daban-daban da su ka kai wannan adadin. Daga bisani an ya zama wajibi a janye wasu abubuwan a ciki don yanzu an daina yayin su kamar amfani da akwatin talabijin marar kala da kuma shigowar sabbin abubuwan da a can baya babu su kamar sayan damar shiga yanar gizo. Bayan sabuwar bitar an ƙara yawan abubuwan nan da a hukumance a ke kira CONSUMAR PRICING INDEɗ CPI da a ka cilla yawan su zuwa 960. Yanzu da waɗannan sabbin abubuwan a ke amfani wajen samar da sabon mizanin da a ke duba tattalin arzikin na Nijeriya. Haƙiƙa lamuran tattalin arziki na da sarkakiyar da sai masana sun yi ƙarin bayani ko fashin baki kafin a fahimce su sarai. Zai zama ba abu mai saukin amincewar akasarin jama’a ba da ke fuskantar tsadar farashin kayan masarufi su gane cigaban alƙaluman mizanin tattalin arzikin ƙasa. Idan a ka ce an samu nasara alhali ba su ga hakan a tukunyar su ta kan murhu ba ba za su lamunta ba. Wasu kuma masu ma ilimin boko kan ƙalubalanci shirin na sabunta mizanin REBASING da tambayar amfanin yin hakan yayin da kasa ke cikin ƙuncin rayuwa na tsadar farashi da ya haura kashi 34%. A nan wannan na nuna har dai ba a ga sauƙin rayuwa ba to a tabaron masu wannan tunani ba amfanin sake yin wannan bitar. Ya zama mai muhimmanci wajen manema labaru su bi diddigin wannan lamarin don fito da yadda lamarin ya ke don samar da wayar da kan al’umma. Misali kowa zai iya shiga kotu alƙali ya yanke hukunci amma ba dukkan mu za mu fahimta ba sai lauyoyi sun yi fashin baki. A kowane ɓangare a na iya samun abubuwa da ke buƙatar karin bayani don kowa ya gane filla-filla. Yau da gobe don yanda kafafen labaru ke ɗauko ƙarin bayani kan abubuwan ƙasa a kan fahimci muhimman abubuwan da ke gudana. A gurguje ma zan je ’yan Nijeriya ko ma waɗanda ba su yi ilimin makarnta ba kan gane bambancin salon mulkin soja mai amfani da dokar soja DECREE da kuma farar hula da ke aiki da tsarin mulki. Ko a farar hular Nijeriya ta fara da tsarin shugaba da firaminista kamar yadda wasu ƙasashen turai ke yi. In an tuna bayan samun ‘yanci gabanin juyin mulkin 15 ga Janairun 1966 Nijeriya ta jarraba irin wanann salon na mulkin farar hula. Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa ke matsayin firaminista yayin da Chief Nnamdi Azikiwe ke zama shugaban ƙasa. Juyin mulkin ya kawo gwamnatin soja ta farko ƙarƙashin Janar Aguiyi Ironsi. Nijeriya ba ta sake samun damar dawowa ƙarƙashin mulkin farar hula ba sai a 1979 inda marigayi Alhaji Shehu Usman Shagari ya zama shugaban ƙasa mai cikekken ikon zartarwa kamar yadda a ke yi a Amurka.

Yanu za mu koma kan sabbin abubuwan da hukumar ta NBS ƙarƙashin jagorancin Prince Adeyemi Adeniran ke shirin shigo da su mizanin da su ka haɗa da hada-hadar kuɗi a ɓangaren miyagun kwayoyi, hakar ma’adinai ba da izini ba, satar man fetur da kuma mata masu yawon gantali. Labarin neman shigo da waɗannan abubuwa ya kawo martanin shin a yanzu gwamnati ta halata safarar ƙwayoyi ne ko ƙaruwanci? Mutane da dama sun soki wannan shiri da ya zama mai muhimmanci a gano yaya lamarin nan ya ke ne. Wato gaskiyar magana hanya ce ta tattara dukkan bayanan hada-hadar kuɗi na ƙasa ta kyakkyawa ko mummunar hanya. Ba yadda za a yi a kore cewa akwai kuɗi daga waɗannan sassan da ke yawo a kasa. Ta hanyar tattara bayanan ƙididdiga ne za a gano adadin kuɗin da tasirin su a tattalin arziki. Akwai wasu ƙasashe a turai da wasu daga waɗannan abubuwan da a ke son kawowa ba su saɓa wa doka ba. A nan Nijeriya ko abubuwan sun yi karantsaye ga doka amma dai su na gudana a ɓoye ko a bayan fage kuma a na hada-hadar maƙudan kuɗi ta waɗannan hanyoyin. Gwamnati na dogara ga samun bayanai daga hukumar ƙididdiga don tsare-tsaren tattalin arziki. Ya zama lallai a samu bayanai na gaskiya kuma aƙalla su shafi dukkan sassa. Kaucewa wasu sassan waɗanda akwai safarar da ta shafi kuɗi masu yawa na kawo nakasu wajen tsare-tsare. Hatta masu zuba hannun jari na ƙetare na buƙatar bayanai daga NBS don sanin yanda za su gudanar da harkokin su. Ta hanyar bayanan ƙididdiga an san yawan layukan salula da ‘yan Nijeriya ke amfani da su da ma ko nawa a kan kashe a kullum wajen tu’ammali da sadarwa. Hukumar kula da kamfanonin sadarwa NCC ta amincewa kamfanonin sadarwa su ƙara kuɗin kiran waya da sauran hidima da kashi 50% duk da sun nemi ƙarin kashi 100%. Bayanan ƙididdiga na sanin adadin kuɗin da kamfanonin ke samu da kuma ko nawa za a ba su damar karawa don su samu ribar da ba ta wuce ƙa’ida ba kuma a biya mu su buƙatar cigaba da aiki a Nijeriya maimakon a bar su su kaura koma su durƙushe don yadda tattalin arziki ke sauyawa a kasuwa.

Wani abun la’akari da shi shi ne raguwar darajar Naira kan dala da yadda Nijeriya ke shigo da akasarin abubuwan da ta ke buƙata daga ƙetare. Idan a ka samu dawowar darajar Naira kuma ƙasar na iya samarwa muhimman kayan da ‘yan kasa ke buƙata a cikin gida za ka ga bunƙasar arzikin da jin tasirin saukin rayuwa a lokaci guda. Ta hanyar haka mizanin jama’a na mu gani a kasa zai yi amfani. Masana tattalin arzikin na shawartar gwamnatin Nijeriya ta rika amfani da Naira wajen biyan kamfanonin ƙetare da ke gudanar da kwangila maimakon amfani da dala. Akwai abubuwa da duk ƙarancin kuɗin shiga da mutum ke samu sai ya yi gwagwarmayar neman su kuma su din ma sai an sa su a ƙididdiga don a gane wane abu ne mutane su ka fi buƙata kuma wanne ne a ciki su ke iya saya. Abubuwan wajibin sun haɗa da abinci, abin sha, sutura da muhalli. Duk rashin dadin abinci ya zama wajibi mai rai ya samu rabon sa. Duk rashin tsabtar ruwa dole mutum ya sha. Duk yagewar sutura mai hankali na buƙata ko da kuwa ganye zai tsinka ya rufe tsairaicin sa. Muhalli kuwa ko a ƙarƙashin gada mutum zai say a samu inda zai sanya hakarkarin sa ya huta. Ta hanyar samun bayanan ƙididdiga gwamnati za ta san yanda ‘yan ƙasa ke rayuwa tsakanin masu sukuni da wadanda ke rayuwar hannu baka hannu kwarya. ƙasa na buƙatar masana masu gaskiya da kwazo da za su riƙa gano alƙaluman bayanai ba tare da duba muradun masu shugabanci fiye da na jama’a ba. Shugaba mai sanin ya kamata kan duba alƙaluman don gyara inda ya dace da ɗaukar matakai don sauya hanya daga marar ɓullewa zuwa mai ɓullewa. ƙasa ba ta nasara daga shaci faɗi ko alƙaluman kitaburra’asi. Duk wata hukumar NBS kan fitar da alkaluman yanda tattalin arzikiya ke musamman ɓangaren farashin muhimman kayan masarufi. A kan fitar da alƙaluman bayan dauko bayanai daga birane da karkara. Hanyoyin tara bayanai na da yawa bisa kwarewa irin ta jami’an ƙididdiga. Koyaushe za a yi tsammani alkaluman ba 100% ba su zama daidai ba to aƙalla ya zama nakasun bai bata muradin haƙiƙanin yanda lamura su ke a ƙasa ba.

Kammalawa;

Duk sabon abu da ya fito a kasa akwai buƙatar duba ciki da bayan sa da sauraron bayanan ƙwararru don gane yadda lamura su ke. Hakanan duk waɗanda haƙƙin jagoranci ya ke kan su ya zama wajibi su riƙa amfani da alƙaluman ƙididdiga don tsarawa jama’a kasafin kuɗi ko ababen more rayuwa. Nijeriya na da arziki da kowa zai iya cin gajiya in an samu bayanai na haƙiƙa da aiwatar da sakamakon bayanan.

By ukarofi