Dokar Haraji: CNG ta nemi mahukunta su kiyayi masu son zuciya

Spread the love

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Ƙungiyar Gamayyar Al’ummar Arewacin Najeriya (CNG) ta ƙalubalanci ƴaƴan majalisun dokoki na tarayya da cewa duk waɗanda suka ƙi bayar da gudunmawar da ta dace wajen yin fatali da tanaɗe-tanaɗen son zuciya da ke cikin dokoki na sauya fasalin haraji da Shugaban ƙasa ya ƙiƙira, su kwana da sanin sun zalunci ƙasa.

Kodinetan ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Jamilu Aliyu Charanchi a wata ganawa da manema labarai a garin Bauchi, ya ce babu wani dalili a yanzu da al’umma ta ke ɗanɗana wahalhalun rayuwa ace za a ƙara kuɗaɗen haraji, yana mai cewa wannan ƙudirorin na gwamnati zalunci ne da ake nufin yi domin daɗaɗa wa wasu mutane ko biyan wata buƙata ta son zuciya.

“Kuma yaya ma za a ce saboda Bola Ahmed Tinubu domin tun lokacin da ya yi Gwamnan Legas zuwa yau, tattalin arziƙin wancan jiha take hannunsa, kuma sai abinda ya ke nufi za a aiwatar a Legas, ace sai yayi wa Najeriya makamancin wancan mulkin, ‘yan Najeriya ala-tilas su kasance bayi?”

Ƙungiyar, ta kuma sake jan kunnen rashin yarda da cire haraji daga cikin kuɗaɗen gado na mamaci, tana mai cewar, yin hakan ya saɓa wa tanade-tanaden addinin Musulunci, kuma tantagaryar zalunci ne ga magada ko masu gado.

“Wannan ƙungiya ta gamayyar arewacin Najeriya tana bisa ƙudirin zage damtse domin tabbatar da cewa, dukkan wani lamari da bai yi wa al’umma daidai ba, duk abu da zai cuci al’ummar Najeriya, dukkan wani abu da zai ƙarawa al’umma wahala, za mu yaƙe shi kamar yadda doka ta tanadar. Idan Allah ya yarda, babu gudu, babu ja da baya, kuma wannan ƙungiya tana yine domin al’umma, domin yankin arewa, kuma domin ƙasar Najeriya”, inji Kwamared.

“Gwamnoni sun yi iyakar tasu iyawar, kuma mu na jinjina masu akan nasu ƙoƙarin, amma bai isa ba, shi yasa muke kira ga ‘yan majalisa waɗanda dokokin yin gyara wa tsarin tattara haraji yake gaban su da su yi abinda ya dace ga al’umma.”

Charanchi ya ƙara da cewa, “Waɗannan dokoki ma, ba an yi su saboda al’umma ba, an fake da su ne domin a qirqiro wannan hukuma mai zaman kanta da ake yin da’awar zata ke tattara kuɗaɗen harajin ƙasar nan. Ana biyan ta ladan kashi 13 cikin 100 a duk kuɗaɗen da ta tattara da zummar a arzurta mutum ɗaya tak, gungu ko kuma zuriyar wani.”

“A wannan duniya da muke ciki, wacce Tinubu yazo ya janye tallafin man fetur, al’ummar Najeriya ta shiga cikin halin ha’ula’i, farashin litar mai ya tashi daga N300 zuwa fiye da N1000; yayi rifom akan canjin kuɗaɗe inda canjin dala ɗaya zuwa naira bai fice N500 ba, ya tashi zuwa N2,000; yayi rifom a sufurin jeragen sama, aka wayi gari kuɗin tikitin jirgi yayi hauhawa yadda kuɗin zuwa Abuja daga Bauchi ya tashi kamar kana biyan kuɗin zuwa Dubai ne ko Saudiyya. Ya yi rifom a food security, farashin buhun shinkafa ya tashi daga N30, 000  zuwa fiye da N100,000,’

“Haka-zalika Shugaba Tinubu yayi rifom a bangaren ilimi, aka wayi ɗalibai masu yawa ba su iya biyan kuɗin karatu, waɗanda suka iya biyan kuɗaɗen karatun, ba su iya cin abinci sau uku a wuni guda, ɗaliban da suke cin abinci sau uku a wuni, idan sun gama karatun, ba su da wata madafar rayuwa; yayi rifom a ɓangaren makamashi da cewar, za’a riƙa samun lantarki na awowi 20 a rana, aka wayi gari ana samun wutar na awa ɗaya ko biyu; ta yaya ɗan Najeriya yake tunani akwai wata manufa da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta bijiro da shi wanda ‘yan Najeriya za su yi da’awar akwai alfanu a ciki? wanda al’umma za ta yarda dashi, ta ce sami’naa-wa’aɗa’ana, babu shi”, inji Charanchi.

By Babaji