An nemi ƙungiyar haɗa kan yankin Funtua ta shirya taron masu ruwa da tsaki

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan harkokin kiwon lafiya na Jihar Katsina Hon. Musa Adamu Funtua ya yi kira ga sabuwar ƙungiyar haɗin kan yankin Funtua da ta duba yiwuwar shirya taron masu ruwa da tsaki a garin Funtua.

Hon. Musa Adamu ya yi wannan kiran a lokacin da shugabanin ƙungiyar suka kai masa ziyarar ban girma a matsayin sa na ɗaya daga cikin uban ƙungiya a ofishin sa da ke Katsina.

Kazalika, ya nuna jin daɗin sa akan yadda aka kafa wannan ƙungiya, wanda ya ce an daɗe ana sa ran samun irin wannan ƙungiya domin haɗa kan al’umma musamman mutanen ƙararmar hukumar Funtua.

Hon. Musa Adamu Ɗan Kafin Katsina na ɗaya wanda ya bayyana Funtua a matsayin gari da ke da tarihin yin biyayya ga shugabanni da sanin addini tun lokacin jihadin Shehu Usman Ɗanfodiyo a yankin Arewa.

“Idan muka duba zamu ga cewa Funtua tana nan rike da matsayin ta na cibiyar hada-hada da kasuwanci wanda ta baiwa kowa damar shi.

By ukarofi