Jirgin Max Air mai lamba NGL1649, Boeing 737 mai lamba 5N-ADB, ɗauke da fasinjoji 119 da ma’aikata shida, ya gamu da haɗari kwatsam a lokacin da ya ke ƙokarin tashi a filin jirgin Yola a yammacin Lahadi.
A wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a , Bimbo Oladeji, ya fitar, jirgin ya samu matsala ne bayan an bashi damar tashi shi daga filin tashi da saukar jiragen sama na Yola a jihar Adamawa, kan hanyarsa ta zuwa Abuja.
A cewar sanarwar, “Lokacin da ake shirin tashi, an ji ƙara mai karfi, wanda aka gano cewa tayoyi ne na baya suka fashe. Wanda hakan yayi sanadiyar jirgin ya kasa tashi.
“Abin farin ciki, ba a sami rauni ba. A yau ne wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar na NSIB, Kyaftin Alex Badeh Jr. za ta ziyarci inda lamarin ya faru domin gudanar da bincike,” Oladeji ya bayyana.
