Gwamnatin Katsina ta ƙirƙiro dokar Iddah ga zawarawa

Spread the love

Gwamnatin jihar Katsina ta ɓullo da dokar Iddah, domin baiwa mata ma’aikatan gwamnati damar zama a gida na tsawon wata huɗu da kwana goma idan sun rasa mazajensu.

A musulunce ana yin iddah lokacin da mace ta rasa mijinta.

Gabatar da sabuwar dokar ya biyo bayan wani ƙuduri da Majalisar Dokokin jihar ta gabatar, inda ta buƙaci gwamnatin jihar da ta duba batun wa’adin Iddah wanda hukumar zartaswa ta amince da shi, tare da yin aiki da shawarwarin da ‘yan majalisar zartaswa suka gabatar.

Shugaban ma’aikatan Jihar Katsina, Alhaji Falalu Bawale ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.

Ya kuma ƙara da cewa, tuni aka fitar da sanarwa ga dukkan ma’aikatu da hukumomin jihar domin baiwa jami’an mata damar gudanar da idda a lokacin da buƙatar hakan ta taso.

By ukarofi