Daga USMAN KAROFI a Abuja
Rundunar haɗin gwiwa a yankin Arewa maso Gabas mai suna ” Operation Haɗin Kai”, ta ceto wata ‘yar Chibok daga dajin Sambisa a Jihar Borno.
Kwamandan rundunar, Manjo Janar Waheed Shuaibu ne ya bayyana haka a lokacin da yake miƙa ta da ‘ya’yanta biyu ga gwamnatin Jihar Borno a unguwar Maimalari da ke Maiduguri, ranar Litinin.
A cewarsa, Ehi Abdul, mai shekaru 27, ta auri wani fitaccen dan ta’adda, Abu Dada a Gwoza a shekarar 2014, ya kuma tsere zuwa ƙasar Senegal.
Wani sashe na rundunar ‘Operation Haɗin Kai’ da ke dajin Sambisa ne suka ceto Ehi da ‘ya’yanta guda biyu a wani samame da suka kai.
