Ba kowacce mace za ta jure yin aiki tsakanin maza ba – Dr. Amina Abdul

Spread the love

Daga ABUBAKAR A. BOLARI, a Gombe

Hajiya (Dokta) Amina Haruna Abdul, Basarakiya ce mai riƙe da Hagalare ta Wakiliyar Tula, ƙwararriya ce kuma tsohuwar malama ce a kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya da ke Gombe, wato Federal Collage of Education (T). Ta yi wallafe-wallafe da dama na ƙasidu dan amfanin ɗalibai a kwalejojin ilimi da na jami’oi.

Dokta Amina ta share kimanin shekaru arba’in tana koyarwa, ta kuma fara koyarwa ne tun daga matakin malamar makarantar firamare ta koma sakandare ta kuma koma Kwalejin Ilimi na Gwamnatin Tarayya, sannan yanzu haka ita ce koodinatar shirin nan na samarwa ‘ya’ya mata ilimi daga Tushe, wato AGILE a Jihar Gombe.

Ku biyo mu, domin jin yadda tattaunawa tsakanin ta da wakilinmu ta kasance. A sha karatu lafiya;

MANHAJA: Ko za ki gaya wa masu karatu taƙaitaccen tarihinki?

DOKTA AMINA: Sunana Dokta Amina Haruna Abdul, ni ‘yar asalin Ƙabilar Tula ce daga Ƙaramar Hukumar Kaltungo a Jihar Gombe. A garin Tula aka haife ni, a can na yi ƙuruciya ta har na girma, iyayena suka sani a makarantar firamare ta Baule/ Gadau a shekarar 1966 zuwa 1971.

Bayan na kammala sai na tafi makarantar sakandaren ‘yan mata ta garin Azare a Jihar Bauchi, wato WTC, inda na samu takardar shaidar karatu ta grade II a shekarar 1972 zuwa shekara ta 1976. Bayan na gama sai na samu nasarar shiga kwalejin ilimi ta horar da ɗalibai ta COE Collage of Education Azare, inda na samu takardar shaidar karatu ta NCE a shekarar 1979 zuwa 1982. Sai na tafi hidimar ƙasa a tsakanin shekarar 1982 zuwa 1983 a garin Bauchi, domin a wancan lokacin idan mutum ya gama karatun sa na NCE zai yi hidimar ƙasa kamar yadda masu digiri suke yi a yanzu. 

Bayan nan sai na tafi Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, a shekarar 1984, na gama a shekarar 1986, inda na karanta ‘Home Economics’ wato yadda ake tattalin gida. Sai kuma na yi ‘masters digiri a jami’ar Jos, wato digiri na biyu a shekarar 1992 zuwa 1998 inda na karanta ‘Guidance and Counseling’, wato yadda ake koyawa yara tarbiyya. 

Sai kuma a shekara ta 2004 na karanta kwamfuta, wato na’ura mai ƙwaƙwalwa a nan Kwalejin ilimi na horar da dalibai ta FCE (T) Gombe, inda nake koyarwa. Sannan na yi digirin digirgir, wato PHD a ɓangaren yadda ake tattalin gida na ‘Home Economics’ a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Ko yaushe Dakta ta fara aiki kuma a ina? 

Na fara aikin gwamnati ne a matsayin malamar makaranta a firamare ta Yayu da ke garin Katagum a Jihar Bauchi, a shekarar 1976 zuwa shekara ta 1977. Daga nan sai na koma firamare ta St, Judes da ke garin Legas a shekara ta 1977 zuwa 1979. Daga nan sai na koma makarantar sakandaren ‘yan mata ta garin Azare a Jihar Bauchi a tsakanin shekara ta 1982 zuwa 1983 a lokacin da nake yiwa ƙasa hidima.

Bayan nan sai na koma WTC Azare daga shekara ta 1983 zuwa shekarar 1986, ina wannan kwalejin ta ‘yan mata sai na koma koyarwa a Kwalejin Ilimi ta garin Azare, COE a shekarar 1986 zuwa shekara ta 1998 lokacin da na dawo nan kwalejin ilimi ta horar da ɗalibai ta gwamnatin tarayya wato FCE (T) Gombe daga shekarar ta 1998 zuwa yau.

Wacce nasara ki ka samu a lokacin da ki ke koyarwa?

A gaskiya kasancewa ta malamar makaranta na samu nasarar koyar da mata yadda za su yi zaman aure da mazajensu da kuma yanayin zamantakewa na rayuwa saboda wasu matan mazajensu ba sa barinsu su shiga makaranta, na kuma shiga kwamitoci daban-daban na harkar mata don ganin na kare haƙƙoƙinsu. Wannan ma nasara ce.

Ko kin fuskanci ƙalubale?

Kowanne irin aiki gaskiya akwai ƙalubale musamman ma kina mace wajen haɗa aikin ki na ‘ya mace a cikin maza, akwai babban ƙalubale saboda ba kowacce mace ce za ta iya daurewa na yin aiki a tsakanin maza ba, ga kuma haɗa ayyukan gida da na ofis ga tarbiyyar yara idan mace ba ta yi sa’a ba sai kaga aure ya mutu.

Sannan kuma idan mace tana aiki amma ba ta yi sa’ar mijin da zai dinga ba ta shawarwari da goyon baya ba za ta fuskanci ƙalubale da yawa. Har yanzu kuma akwai irin mazajen da suke ganin ba za su iya yin aiki a ƙarƙashin mace ba, idan Allah ya ɗaukaka ta ya ba ta shugabanci saboda suna ganin ke mace ce suna da kamar ki a gida kaga dole matsala za ta taso.

Ya batun iyali ?   

Alhamdulillahi godiya ga Allah, ban samu haihuwa da wuri ba, amma duk da haka Allah ya albarkace ni da ‘ya’ya biyu, namiji da mace.

Ko kina cikin wata ƙungiya?

Na taɓa zama mamba da kuma shugabancin ƙungiyoyi masu yawa, amma kaɗan daga cikin su su ne; kwamitin ilimin kwamfuta na FCE Gombe, Sakatariya ta ƙungiyar ma’aikata masu koyarwa na kwalejin ilimi wato (COEASU), shugabar mata ta kwalejin ilimi (WICE) Women in Collage of Education ta Gombe, da kuma shugabar sashin kwalejin ilimi na koyar da sana’oi na Kwalejin ilimin na Gombe da dai sauransu.

Ko Dakta ta taɓa ziyartar ƙasashen waje?

Babni da shawa’ar zuwa wata ƙasa a duniya, saboda ba sa gaba na, amma dai na je Saudiyya kuma ina da sha’awar sake komawa nan gaba.

Wane abu ki ka fi son a dinga tunaki da shi ko bayan ranki?

A gaskiya abinda na fi son a dinga tunani da shi shi ne. duk inda ɗalibina ya ganni ya bani shaida ta gari kasancewa ta daɗaɗɗiyar malamar makaranta kuma zan ji daɗi ni kaina inna ga ance ga ɗalibin da na koyar da shi ya zama wani abu a rayuwa. 

Yanzu haka cikin irin ɗalibaina akwai waɗanda suka kai wani matsayi a ƙasar nan da yawa, akwai tsohuwar kwamandar hukumar tsaro ta farin kaya ta Jihar Gombe, wato Ciɓil defence Hajiya Altine Sani Umar ɗalibata ce a Azare. Wannan ma abin alfahari ne gare ni. Akwai ire-iren su da yawa.

Menene burinki a rayuwa?

Idan na yi ritaya na bar aiki ba ni da burin yin siyasa kamar yadda waɗansu suke ba ni shawarar shiga siyasa, sai dai ina da buri na buɗe makaranta ina karantar da yaran unguwa da nawa koda na bar aiki saboda aikin malamta aiki ne na sadaukar da kai.

Kin taɓa samun lambar yabo?

Na samu lambar yabo na ɗalibar da ta fi fice a lokacin da nake kwalejin ilimi na garin Zariya a shekarar 1986, sannan ƙungiyar ɗalibai ta garin Kaltungo da Shongom reshen jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke garin Bauchi sun karramani da lambar yabo na wacce take taimaka wa harkar ilimi a yankin Masarautar Kaltungo, na kuma samu lambar yabo na yadda na gudanar da shugabanci na a lokacin da nake shugaba ta shiyar Arewa maso gabas na WICE (Women in College of Education) na Yola.

Mece ce shawarar ki ga mata?

A matsayina ta uwa ina mai bai wa ‘yan uwana iyaye mata shawara na su daure su dinga sanya ‘ya’yansu mata a makarantar boko inda za su sami ilimin zamani bayan na addini da suke yi da zai kai su ga dogaro da kansu koda bayan sun yi aure ne, ta hanyar ragewa mazajensu ɗawainiyar gida.

Ba ilimin addini ne kaɗai ne abin nema ga ‘ya’ya mata ba, dukka harda na boko, saboda a gaskiya jahilci ne a bar mata kara zube ba ilimi sai talla ko aikin gona, wato Barema a lokutan damuna da kaka’ah, domin idan aka ce yau mace ba ta da ilimi koda tarbiyar ‘ya’yan ta ba ta san ta inda za ta fara ba, sannan kuma yana da kyau iyaye su gaggauta gane cewa hana ‘ya mace karatu sai tallace-tallace shi ya kan jefa rayuwarsu cikin bala’i domin ta hanyar talla ne mafi yawan su suke jawowa iyayensu takaici da zarar sun sami ciki a layi, da fatan Allah ya sa mu dace. 

Sannnan kasancewa ta koodinata ta shirin AGILE muna iya ƙoƙarinmu tare da haɗin gwiwar Gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya, wajen tabbatar da shirin ya ɗore an kuma dawo da yaran da babsa zuwa makaranta sun koma ana ɗan ba su wani alawu-alawus na karatu dan ƙarfafa musu gwiwa tare da iyayensu.

By ukarofi