Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau
Wani matashi mai suna Hassan Ɗan Chanji, ya halaka wata matar aure mai suna Rakiyaya matar Malam Maikuddi a Garin Dambo dake ƙaramar hukumar Bakura a Jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin Malam Tukur Dambo ya shaidawa wakilin mu ta wayar tarho a zantawar sa da Blueprint Manhaja cikin daren nan.
Malam Tukur Dambo ya shaidawa wakilin mu cewar labarin ya faru ne da yammacin yau Laraba bayan da wanda ake zargin da matar da ya halaka su kayi sa’insa na cacar baki a tsakanin su.
“A yayin sa’insar ne, sai ya shiga gida ya ɗauko makami ya shiga saran ta har sai da yaga ta mutu”. A cewar Malam Tukur Dambo
Malam Tukur Dambo ya bayyana cewar daga baya yan uwanta suka ɗauko makamai suka haushi da duka suka kasheshi nan take.
“Yanzu haka dai an garzaya da gawarwakin zuwa babban asibitin Bakura hedikwatar ƙaramar hukumar ta Bakura domin gwaje-gwaje.
Duk ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar ta Zamfara da wakilin mu yayi abun yaci tura a yayin haɗa wannan rahoton.
