Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Tsohon ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyar adawa ta ADC Dr Junaidu Lawal Trader ya faɗawa manema labarai haka a wajan taron jam’iyar a Katsina.
Ya ce matsalolin rashin tsaro, tabbatarwan ilimi ya lalace, harkar noma da tattalin arziki suka sanya mutane ke ruwa zuwa jam’iyar su ta ADC.
“Kowa naji a jikin sa kan haka ne mutane ke neman makoma da ingancin rayuwa a jam’iyar mu ta ADC,”inji Junaidu Trader.
Dr Junaidu ya bayyana cewa ganin irin mashahurai kuma adalan mutanen da suka shiga cikin jam’iyar su yana da tabbacin samun nasara a tafiyar.
Tsohon ɗan takarar wanda kuma tsohon ma’aikacin hukumar bada bashi na duniya (IMF) da bankin Duniya (World Bank) ya ce duk da gwamna Dikko Raɗɗa ya yi ƙoƙari a fannin da dama akwai wuraren da bai taɓa ba “Idan na samu dama zan taɓo wuraren. Yakamata Raɗɗa ya taɓa bai taɓa ba.
Ya kuma soki gwamnatin APC yadda ta fi mai da hankali wajan bada tallafi maimakon gina al’umma ta hanyar samar masu da aiki yi da koya masu sana’ar da zasu tsaya da ƙarfin su .
Mayan mutanen da suka halarci taron sun haɗa da tsohon darakta janaral na hukumar tsaron farin kaya Lawal Musa Daura da madugun adawa Mustapha Muhammad Inuwa da sauran su.
