
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami SAN, ka iya ɗaukar tsawon lokaci a hannun Hukumar tsaron ta farin kaya (DSS), kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Majiyoyi masu yawa daga ɓangaren tsaro sun ce Malami na fuskantar tsarewa ta dogon lokaci, yayin da DSS ke kokarin samun izinin kotu domin cigaba da riƙe shi har sai an kammala binciken da ake yi a kansa.
Wannan sabuwar taƙaddamar ta fara ne a ranar Litinin, lokacin da jami’an DSS suka kama Malami jim-kaɗan bayan ya cika sharuɗɗan belinsa kuma aka sake shi daga gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja.
Hakan na zuwa ne tun bayan tsare shi a farkon watan Disambar 2025 bisa zargin da hukumar EFCC ta shigar da shi a kai.
Majiyoyin tsaro sun ce DSS na neman umarnin kotu ne domin tsawaita tsarewarsa, inda suka alaƙanta hakan da sahihanci da sarkakiyar binciken, wanda ake sa ran zai ɗauki tsawon watanni da dama.
A cewar majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin, ana yi wa Malami tambayoyi masu tsauri kan yadda ya tafiyar da jerin sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Nijeriya da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta fitar.
“Akwai batutuwa da dama da ake yi masa tambayoyi a kai. Daya daga ciki shi ne yadda aka tafiyar da jerin sunayen masu daukar nauyin ta’addanci da UAE ta fitar a shekarar 2021, da kuma wasu batutuwa da suka shafi masu daukar nauyin ta’addanci a lokacin da yake antoni janar”, inji majiyar.
Tun a shekarar 2021 ne hukumomin UAE suka ambaci ’yan Nijeriya shida da ke da alaƙa da kungiyar ’yan ta’addar Boko Haram a matsayin masu ɗaukar nauyin ta’addanci a ƙasar.
Majalisar Ministocin UAE ta fitar da Kuduri na 83 na 2021, inda ta sanya mutane 38 da ƙungiyoyi 15 a jerin waɗanda ake zargi da tallafa wa Boko Haram da sauran ayyukan ta’addanci musamman a yankin Arewa ta Yamma.
‘Yan Nijeriya a jerin sunayen sun haɗa da: Abdurrahman Ado Musa, Salihu Yusuf Adamu, Bashir Ali Yusuf, Muhammed Ibrahim Isa, Ibrahim Ali Alhassan da Surajo Abubakar Muhammad.
