Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta tsige Abure, ta umarci INEC ta tabbatar da tsagin Nenadi a shugabancin LP

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja, ta tsige Mista Julius Abure daga muƙaminsa na shugabancin Jam’iyyar LP.

Yayin sanar da haka a yau Laraba, kotun ta kuma sanar da cewa daga yanzu Sanata Esther Nenadi Usman, wadda tsohuwar ministar kuɗi ce, ita ce halastacciyar shugabar jam’iyyar.

Mai Shari’a Peter Lifu a yayin gabatar da shari’ar, ya ce ya yi hukuncin ne bisa la’akari da matsayar Kotun Ƙoli ta ranar 4 ga watan Afrilun 2025 wadda ta ayyana hakan.

Don haka babbar kotun ta umarci Hukumar Zaɓe (INEC) da ta tabbatar da kwamitin riƙo ƙarƙashin jagorancin Sanata Nenadi Usman a matsayin halastaccen jagorancin LP har zuwa lokacin da za a yi babban taron jam’iyyar.

A cewar alƙalin, hujjojin da aka gabatar masa sun nuna cewa wa’adin Abure a matsayin shugaban jam’iyya ya ƙare tun da jimawa.

A nasa ɓangaren, kwamitin zartarwar (NEC) jam’iyyar bayan shawarwari, ya yanke hukuncin tsige Abure a matsayin shugaban.

Tuni jam’iyyar ta shirya sunayen mutum 29 na kwamitin riƙon da za su yi aiki da tsohuwar ministar a matsayin shugabar LP.

By Babaji