
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da rahotannin cewa ‘yan bindiga sun yi awon-gaba da mutane da dama na ƙauyen Kurmin Wali da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru a jihar Kaduna bayan da fari reshen rundunar na Kaduna ya ƙaryata.
A wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Talata daga jami’in hulɗa da jama’arta, ACP Olumuyiwa Adejobi ta Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, rundunar ta ce harin ya auku ne a ranar Lahadi, inda ta ce tuni aka tura jami’ai domin ƙaddamar da atisayen ceto waɗanda al’amarin ya shafa.
Ya bayyana cewa, da fari ‘yan sanda da gwamnatin Kaduna sun musanta rahotannin ne domin kauce wa haddasa firgici acikin al’umma yayin da ake ƙoƙarin tabbatar da rahoton, zancen da ƙungiyoyin al’umma da na jagororin addini suka riƙa suka.
Duk da cewa rundunar ba ta bayyana haƙiƙanin adadin waɗanda aka sace ba, majiyoyi da dama sun ce harin na ɗaya daga cikin mafi girma da aka kai a ‘yan watannin nan.
Wani ɗan majalisar Kaduna mai suna Usman Ɗanlami Stingo ya shaida wa manema labarai cewa aƙalla mutanen da aka yi garkuwar da su za su kai 168 yayin ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) a Arewa ta ce aƙalla masu ibada 172 ne aka sace waɗanda daga ciki guda tara suka tsere.
A cewar shaidu da rahoton ‘yan sanda, al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:25 na ranar Lahadi a lokacin da mutanen suke tsaka da ibada a Cocin ECWA da cocinan Cherubim da Seraphim na 1 da 2 a Kurmin Wali.
Rahoton ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun je yankin ne ɗauke da wasu muggan makamai,wanda hakan ya sanya mutane da dama tserewa zuwa dazukan da ke kewayen yankin. A yayin haka ne suka yi nasarar awon-gaba da masu yawa daga cikinsu.
Ga jaddawalin waɗanda aka sacen kamar yadda masu sharhi suka bayyana na wasu daga cikin iyalai shida:
Jonathan – mutane 12
Amos – 13 mutane
Markus/Makudi – 10
Ishaya da Danisa – 7 ga kowannensu
Bawa – mutane 6
Danjuma da Musa – 5 ga kowane gida.
Sauran sun haɗa da:
- Zahaya Joshua
- Nabilah Makudi
- Hajara Makudi
- Rebecca Hosea
- Ahmad Ahmad
- Liyu Ezekiel
- Vivian Ezekiel
- Goodluck Ezekiel
- Beauty Ezekiel
- Matina Maiyashi
- Bridget Maiyashi
- Vivian Linus
- Mary Amos
- Hamid Amos
- Patricia Amos
- Hamisu Amos
- Luka Amos
- Tacy Amos
- Cynthia Amos (guessed)
- Mercy Isaac
- Augustine Makudi
- Matthew Samaila
- Adam Musa
- Malika Sule
- Abu Ahmad
- Hussein Lucky (guessed)
- Akinyi Sadiu
- Dangata Amos
- Helen Jonathan
- Asinwa Jonathan
- Faith Joseph
- Gloria Kennet
- Happiness Danisa
- Fidelis Jacob
- Tobias Markus
- Istu Paul
- Hassana Paul
- Charity Chindo
- Christiana Danisa
- Everest Danima
- Thomas Philip
- Catrina Danbosi
- Halima Hassan
- Hassan Lukumi
- Mary Sadiu
- Franca John
- Henry Danbiyi
- Genesis Lawal
- Ayuba Lawal
- Solomon Ayuba
- Theophilus Danlami (guessed)
- Charles Sambo
- Rahila Charles
- Gambo Danisa
- Talent Danisa
- Nehemiah Danjuma
- Maijima Shekarau
- Matina Maijima
- Laraba Maijima
- Musa Danjuma
- Ishaya Danima
- Lulu Danisa
- Clement Ahmad
- Destiny Ahmad
- Nehemiah Ishaya
- Simon Ishaya
- Nasty Muku
- Helena Joseph
- Joseph Bawa
- Sarah Joseph
- Bulus Mariya
- Musa Samaila
- Bulus Bawa
- Halima Bawa
- Beture Hosea
- Sati Hosea
- Titus John
- Dogara Bawa
- Lories Bawa
- Adamu Aminu
- Ezekiel Adamu
- Tenah Markus
- Patricio Bawa
- Janet Tsuda
- Amina Danjuma
- Sandra Danbosi
- Bridget Sunday
- Saphat Innocent (baƙuwa)
- Alex Sunday
- Beauty Peter
- Samisa Paul
- Joy Joseph
- Methole Johanna
- Genesis Johanna
- Maria Johanna
- Merozdu Adonu
- Karimi Jangbe
- Sunday Martela
- Santina Hershinga
- Keuna Michael
- Hassan Bulus
- Marzeta Maisoni
- Mainwa Dominic
- Godwin Karimi
- Amos Akijo
- Nathan Amos
- Joseph Chindo
- Lydia Godwin
- Hamna Maiyangi
- Toletu Maiyangi
- Esther Godday
- Godlive Samson
- Goodluck Aliga
- Madaki Tabawa
- Tabawa Abba
- Tabawa Iyamye
- Samuel Amos
- Daniel Amos
- Deborah Amos
- Ruth Amos
- Emmanuel Danjuma
- Joshua Danjuma
- Rejoice Danisa
- Blessing Danisa
- Ibrahim Lawal
- Zainab Lawal
- Sadiq Ahmad
- Aisha Ahmad
- Yakubu Musa
- Suleiman Musa
- Rahama Musa
- Daniel Jonathan
- Samuel Jonathan
- Peter Jonathan
- Grace Jonathan.
Tuni dai rundunar ‘yan sandan Kaduna ta ce ta fara gudanar da binciken akan al’amarin domin ganin an ceto mutanen cikin aminci.
