An kammala ginin cibiyar Musulunci a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Cibiyar musulunci da gidauniyar Sautus Sunnah Charity Foundation ta gina a Unguwar Kadarko Estate cikin garin Katsina na ɗauke da katafaren masallacin Juma’a, makaranta da gidan liman.

Shugaban ƙungiyar izalatul bidi’a wa iqamatul sunnah Sheikh Yakubu Musa Hassan ya sanar da cewa ana shirye shiryen buɗewa nan ba da jimawa ba.

Sheikh Yakubu Musa wanda har ila yau shine shugaban gidauniyar Sauttus sunnah ya nuna gamsuwa da yadda akai ingantaccen aiki.

Yayi kira ga al’ummar musulmi da su tashi tsaye wajen aikin Allah ta hanyar aiwatar da irin wannan aiki.

Sheikh Yakubu Musa Hassan yayi ta’aziyar rasuwar marigayi Sheikh Habibu Yahaya Ƙaura wanda ya rasu a wani Asibiti da ke Abuja.

Ya bayyana Sheikh Habibu Ƙaura a matsayin malamin da ya sadaukar da rayuwar sa wajen yaɗa addinin Allah.

By ukarofi