Daga USMAN KAROFI
A shekarar da ga gabata, hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta bayyana cewa aƙalla mutane 215 suka rasa rayukansu a sanadin zazzaɓin cutar Lassa. Ga wanda ya ke bibiyar alƙaluman da kuma yanayi na yaɗuwar cutar zai san cewa wannan adadin yawan mutanen da suka rasa rayukansu dole hankali ya tashi. Alƙaluman da suka fito sun nuna cewa an samu waɗanda ake zargi da cutar aƙalla mutum 9389 wanda a cikinsu kuma a tabbatar da mutum 1148 sun kamu da cutar kuma a cikinsu a ka samu mutane 215 da suka rasu wanda yayi dai dai da kaso 18.7%.
Wani abu da nake so mu yi duba a nan shine a wurin mutane da dama don an ce mutum 215 sun rasu a cikin mutum 1148 suna kallon adadin kamar babu yawa. Amma a tsarin kiwon lafiya wannan ba ƙaramin ɓarna ta yi ba. Kuma mutane suna kallon adadin a matsyin lambobi kawai alhali rayukan mutane ne. Shin mun taɓa tsayawa muyi duba da cewa duk cikin mutane 215 kowanne su ‘yan Adam ne masu cike da burika amma kwatsam cutar Lassa ta katse wannan buri? Duk mutum ɗaya da aka rasa, wani uba ne, wata uwa ce, wasu yara ne da aka jima ana nema kafin a samu da dai sauran su.
Rashin tsaftar muhalli, talauci, jinkirin zuwa asibiti, da rashin cikakken bayani sun taimaka wajen yaɗuwar cutar a 2025. Wannan na nuni da cewa cutuka irin su zazzaɓin Lassa za su cigaba da yi mana illa in har ba mu gyara abubuwa da dama da suka shafi zamantakewar mu ta yau da kullum.
Menene cutar Lassa?
Zazzaɓin Lassa cuta ne da ƙwayar cutar lassa virus ke haddasa wa. Wannan cuta tana cikin nau’o’in cuta da a turance a ke kira zoonotic diseases domin za a iya ɗaukar su daga dabbobi zuwa mutane. Cutar na da matuƙar hadari ganin yadda take saurin halaka mutane idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba ko kuma a kai jinkiri wajen zuwa neman lafiya a asibiti. Saboda haɗarin ta, a tsarin sanya idanu da bayar da rahoto na IDSR guideline( Integrated Disease surveillance and response) ya sanya ra a cikin cutukan da an samu ɓullar su a kai rahoto nan take da gaggawa ba tare da jinkiri ba.
Menene alamomin cutar?
Alamomin cutar sun haɗa da zazzaɓi, ciwon jiki, ciwon ciki, amai, ciwon kirji da sauran su. Alamomin da na fara bayyana ne daga kwana 6 zuwa 15 daga ranar da mutum ya kamu da kwayar cutar.
An fi saurin ɗauka daga ɓeraye, daga kashin su ko firsarin su.Don haka ina kira ga mutane da mu jajirce wajen tsaftar muhalli, rufe kayayyakin abinci da bera zai iya shiga ko wasa a kai, sannan mutane da sun ga wani da alamomin cutar ai gaggawar sanar da hukuma.
