Wani mutum ya gamu da ajalinsa a yunƙurin satar mutum-mutumin Agemo

Spread the love

Wani da ake zargin ɓarawo ne mai suna Jeremiah Kosesochi Nwoke ya mutu a lokacin da yake yunƙurin sace mutum-mutumin Agemo da ke unguwar Itoro a Ijebu Ode a jihar Ogun.

Lamarin wanda ya faru da tsakar daren ranar Juma’a, 11 ga Afrilu, 2025, ya girgiza mazauna yankin.

Mutum-mutumin yana tsaye ne a kusa da shataletalen da ke kan hanyar zuwa babban gidan sarauta na Awujale na Ijebuland.

An tattaro cewa marigayin ya yi ƙoƙari da dama a cikin duhu domin ya tumɓuke tare da sace mutum-mutumin.

Sai dai ana zargin marigayin ya tumɓuke wannan mutum-mutumin da aka yi masa lulluɓinda siminti, amma ya mutu kafin ya tafi da shi.

Agemo wani abu ne mai daraja a Ijebu, wanda suka yarda cewa shi ne mai kare yara kuma wanda ke kiyaye makomar Ijebus ta hanyar albarkarsa. Ana karrama shi a wani biki mai suna Agemo Festiɓal.

Bikin yana da nasaba da addinin gargajiya na Afirka, musamman, al’adun gargajiya na Agemo, don haka, batutuwa kamar hana zirga-zirga a wasu lokutan bikin suna faruwa.

Ana gudanar da bikin ne a tsakanin watannin Yuni da Agusta, kuma a tarihi ya zo daidai da girbin masara da manoman Ijebu ke yi.

By ukarofi