Wasu marubutan da suka samu ɗaukaka suna da girman kai –  Fatima Sunusi Rabi’u 

Spread the love

“Sanadin kyautar da aka min a dalilin rubutu na samu jarin sana’ata”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Fatima Sunusi Rabi’u, ba marubuciyar onlayin ba ce kawai, tana daga cikin marubutan da suka wallafa littattafansu a tsarin ɗab’i, har ma suka shiga kasuwa. Bayan kasancewarta ƴar kasuwa, tana matuƙar sha’awar aikin jarida na gidan rediyo. Ta rubuta littattafai da gajerun labarai fiye da goma, kuma har yanzu tana kan cigaba da rubutu. A ganawarta da wakilinmu Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar da ake yi wa laƙabi da Ummu Affan ta bayyana masa burinta na ganin an samu canji a harkar rubutun adabi da kasuwancin littattafan Hausa. A sha karatu lafiya. 

MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki.

FATIMA SUNUSI: Assalamu alaikum. Sunana Fatima Sunusi Rabi’u wacce aka fi sani da Ummu Affan a duniyar rubutu. Ni ɗaliba ce, marubuciya, kuma ƴar kasuwa. Ina kasuwancina a onlayin, ina sayar da maganguna na kamfanin GHT, da kuma kayan yara na gwanjo, da sauransu. Ina zaune a garin Kaduna tare da iyalina.

Ki ba mu tarihin rayuwarki da matakin karatunki.

An haife ni a ranar sha ɗaya ga watan uku shekara ta 1997, a ƙaramar Hukumar Funtua dake Jihar Katsina. Na yi karatuna na firamare a Nadabo Anneɗ Primary School Jantiti, na kammala a 2009. Na tafi sakandire a GGDSS Bakori, inda na kammala ƙaramar sakandire a can, sai kuma rayuwata ta koma garin Kaduna. A nan ne na cigaba da karatuna na babbar sakandire a Maimuna Gwarzo, inda na kammala a 2015. A ɓangaren karatun addini kuma, na yi ilimin addinin Musulunci daidai gwargwado har ma na yi saukar Alƙur’ani Mai Girma. Yanzu haka ina da aure da yara huɗu. Wani dalili mai ƙarfi ya dakatar da karatuna na gaba da sakandire, amma ina da niyya zan koma karatuna a wannan shekarar, in sha Allahu.

Ba mu labarin yadda ƙuruciyarki ta kasance, wacce tarbiyya ki ka samu yayin tasowarki?

Alhamdulillah, an yi ƙiriniya kam daidai gwargwado, musamman ta yadda na fara tasowa a gidan kakanni na, kasan dai yadda riƙon tsofaffi yake. Na yi wasan ƙasa, na yi ‘yar gala-gala da tafa-tafa, kuma na yi tsokana sosai. Mun yi karatun Islamiyya ta dare. Amma cikin godiyar Allah na samu tarbiyya sosai daga iyayena har zuwa kakannina. Haka Hajiyata da ta riƙe ni har zuwa aure, sai dai in ce Allah Ya saka musu da alkhairi, Ya ƙara musu lafiya, amin.

Wanne buri ki ka taso da shi a rayuwarki?

To, na taso da burin son yin karatu mai zurfi sosai, sai dai mahaifina yana da wata ƙa’ida ta aurar da yaransa da wuri, muddin ‘yarsa ta samu miji kuma tana sonsa, ko da kina sakandire ne zai aurar da ke. To, ni ma da na taso da son samun karatu mai yawa, sai kuma na samu rashin ƙwarin gwiwa daga mahaifina. Amma Alhamdulillah, har gobe ina godewa mahaifina saboda ya aurar da ni a lokacin da ya dace, don kowanne uba burinsa ya rabu da ‘ya’yansa lafiya. Kuma na samu mijin da ya fahimce ni, yana kuma ƙarfafa mini gwiwa akan samun ilimi, kamar yadda nake buri. Kuma in sha Allahu, ina da burin na karanci aikin jarida ne, don in riƙa aiki a rediyo, idan na samu damar hakan.

Yaya aka yi ki ka fara sha’awar rubuce-rubuce?

Na kasance mai yawan karance-karance, na yi karatu kamar ba zan bari ba. Har aka zo lokacin da na ji cewa nima fa zan iya rubutawa. Kamar da wasa na samu littafi da biro na fara rubutawa, don lokacin ina gida ba na fita, kasancewar dangina suna gida wato Funtua, ni kuma ina Kaduna. Zaman ni ɗaya da rashin zuwa ko’ina sai gidan Hajiyata kuma surukata, wannan kaɗaicin ne ya sa na fara rubutu a littafi da niyyar zan buga. Sai kwatsam na ga ana rubutu onlayin na ce to, ai nima zan iya ba da gudummawata, sai kawai na fara. Ganin an karɓa daga nan sai na cigaba da yi.

Wane ne ya fara koya miki yadda ake rubutun adabi?

Gaskiya ba wanda ya koya mini, ni da kaina na fara rubutuna. Sai dai kasancewa ta a zauren Aji Na Musamman, dake manhajar WhatsApp, ya sa ni ƙara ilimi sosai, da sanin ƙa’idojin rubutu.

Wanne labari ki ka fara rubutawa, kuma akan mene ne?

Na fara rubuta labarin ‘Uwanin ƙauye’, a Facebook. Labari ne akan wani shahararran ɗan kwallon ƙafa wanda yake ɗaukar kansa da girma da ganin ya fi ƙarfin ya kalli duk wata ƴa mace, ballantana ya ce yana so. Sai kwatsam, ya dawo ya iske mahaifinsa ya zaɓa masa matar aure kuma ‘yar ƙauye. Ya dinga wulaƙanta ta da ganin shi fa ya fi ƙarfin a ce yadda yake ya auri wata ‘yar ƙauye. Sai Allah Ya nuna masa ikonSa na dasa masa ƙaunar Uwani, duk da kuwa ita ɗin ta fito daga ƙauyen ƙayau.

Kawo yanzu kin rubuta cikakken littafi guda nawa? Gajerun labarai nawa?

Na rubuta littattafai a ƙalla goma sha biyar, gajeru kuma, saboda shiga gasa, na rubuta aƙalla goma. Daga cikin dogayen labarai akwai, ‘Uwanin ƙauye’, ‘Cikin Waye?’ ‘Na Yi Gudun Gara’, ‘Ni da Yaya Lameer’, ‘Wanka da Gari’, ‘Baƙar Fura’, ‘Mu Gani A ƙasa’, ‘Rumbun Wasa’, ‘Ginshiƙin Dutse’, ‘Randar Cikin ɗaka’, da sauransu. Daga cikin gajerun labarai kuma akwai, ‘Rukunin Jini’, ‘Idan da Rai’, ‘Cancanta’, da sauransu.

Ki yi mana bitar wasu daga cikin littattafanki da suka yi fice.

To, akwai littafin ‘Ginshiƙin Dutse’, wanda labari ne akan wata hatsabibiyar yarinya, wacce bata jin maganar iyayenta har ma tana wasa da dokokin Allah. Illolin abota da gurɓatattun ƙawaye dake ɓata tarbiyyar da aka daɗe ana ginawa a gida, cin amana, kwaɗayi da kuma rashin godiyar Allah na daga cikin darussan da labarin ke koyarwa.

Sai kuma labarin ‘Baƙar Fura’, wanda ke magana akan wani jajirtaccen ɗan jarida da ya tsaya kai da fata domin tono gaskiyar wasu ɓatagari da suke bada gudunmawa ake satar mutane, inda ya gano ashe har da wani shaƙiƙinsa da bai taɓa tsammanin da hannunsa ba. Labari ne akan masu satar mutane ana ba su kuɗin fansa kuma ya yi bayani akan siyasar zamani.

Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wanne cigaba ta kawo a rayuwarki ta rubutu?

Ni tun da na fara rubutu a ƙungiyar Arewa Writers Association nake, wacce Hauwa S. Zaria ke jagoranta, kuma har yanzu ina cikinta. Ina alfahari da ita sosai, don na koyi abubuwa da yawa a cikinta. Harwayau kuma, ina cikin ƙungiyar mata zalla ta Women Of Words, kuma ita ma daidai gwargwado ana mana bita akan adabi da wasu abubuwan na ƙaruwa da dama.

Kin taɓa shiga wata gasar marubuta? Wacce nasara ki ka samu da wanne labarin?

Alhamdulillah. Na shiga gasanni daban-daban, wasu an samu nasara wasu kuma an faɗi, sai dai ko ita ma faɗuwar tana zuwa ne tare da nasara. Na yi ta ɗaya a Gasar Tambari Writers Association, a shekarar 2021. Sannan na yi ta biyu a Gasar da ƙungiyar Wilaya Writers Association of Nigeria (WIWAN), a shekarar 2022. Na samu nasarar shiga rukunin kusa da na ƙarshe a Gasar Tsangayar Gusau har sau biyu, a 2023 da labarina mai taken ‘Rumbun ƙasa’, da kuma a shekarar 2025 inda labarina ‘Sulallan Gizo’ ya yi zarra a cikin fitattun labaran da aka tantance. Na kuma zama ta ɗaya a Gasar Matasan Marubuta ta Billy Galadanci. Na samu shaidar ƙarramawa a wasu daga ciki da na shiga da dama.

Marubuta da dama suna ɗora littattafan su da ake karantawa a manhajar YouTube, shin ke ma kina da naki zauren ne?

E, Ina da nawa zauren aji YouTube inda ake karanta labaraina, amma bai jima da na fara ba, yanzu ake kan rainonsa. 

Wanne cigaba ki ka samu a dalilin rubutun da ki ke yi?

Gaskiya Alhamdulillah na samu cigaba sosai, kaifafa ƙwaƙwalwata, haɗuwa da mutanen arziƙi samun kyaututtuka na ban mamaki. Akwai wacce silar karatun littafina ta min kyautar da har yau idan na tuna ina samun farinciki saboda na ja jari da kuɗin, silarsu na sayi wasu abubuwan da idan na kalla ina tunawa da wannan abin sosai, kuma ina kallonsa a matsayin cigaban da na samu silar rubutu.

Kin taɓa samun wani ƙalubale a dalilin rubutu, ko saboda hulɗa da marubuta?

Gaskiya ban samu wani ƙalubale da marubuta ba, don duk wanda zan zauna da shi da zuciya ɗaya nake zaune da shi, sai dai kuma idan daga gare shi ne. Amma duk marubuta ina yi musu kallon ‘yan’uwana ne.

ƙalubalen da na samu a rubutu bai wuce na littafin ‘Baƙar Fura’ ba, da yake ana karanta littattafaina a wani gidan rediyo a nan Kaduna to, wacce ke gabatar da shirin ta kira ni a waya cewa sun karɓi labarina za su karanta, sai dai ta duba littafin ta ga ba zai yiwu su karanta ba, sakamakon akwai siyasa a ciki, kuma na nuna wasu halayen ‘yan siyasa da yadda na fito da abin da ake yi ƙarara, kuma na nuna da hannunsu a ciki. Wannan dalilin ya sa daga kan shi ban ƙara rubuta labarin da ya danganci siyasa ba, duk da ina da abin rubutawa sosai akan hakan. Wannan ya zamo mini wani ƙalubale gaskiya.

Shin kina ganin ana samun cigaba a harkar rubutun onlayin?

Gaskiya ana samun cigaba sosai, domin a yanzu za ka sayar da labarinka ba tare da ka buga ba, kuma za ka iya bugawa ka tallata a onlayin duk a saya.

A ganinki wacce hanya ce za a bi a inganta kasuwancin rubutun adabi na onlayin?

ƙirƙirar abubuwa na musamman, da amfani da kafafen sada zumunta wajen tallata rubutunka da haɗa talla da zai ƙayatar da mai saye, kuma ka yi rubutu mai kyau. Idan aka yi haka za a inganta harkar kasuwancin littattafan Hausa na onlayin.

Ana cigaba da samun ƙaruwar marubutan onlayin da ke buga littattafan su a takarda, shin ke ma kina da ra’ayin haka?

E, tabbas ina da ra’ayi. Na ci wata gasa a shekarar 2022, inda na fito cikin mutane biyar da aka buga musu labaransu, bayan wannan na buga wasu littattafaina, ‘Mu Gani A ƙasa’, ‘Wanka Da Gari’, da kuma ‘Baƙar Fura’ wanda shi ne aka buga mini.

Gaya mana marubutan da rubutun su yake burgeki a maza da mata?

A maza akwai  Jibril Adamu Jibrin Rano, sai Abdullahi Hassan Yarima, Yusuf Gumel da Muttaƙa A. Hassan. Sai a mata kuma akwai Khaleesat Haidar, Maman Nurul Huda, Rufaida Umar Ibrahim, da Amira Adam.

Akwai wanda ki ke kwaikwayon salon rubutunta a cikin marubuta?

Gaskiya ba na kwaikwayon salon rubutun kowa, nawa salon nake yi.

Idan za a baki dama wanne sauyi za ki kawo wa harkar rubutu?

Zan kawo sauyi ta hanyar daƙile rubutun batsa, kodayake an samu cigaba abin ya yi baya sosai. Sannan kuma zan ba marubuta shawarar mu riƙa rubuta abubuwan da ke faruwa a rayuwa, mu daina nace wa a jigo guda. Idan mun kaifafa tunani za mu samu labarai da za su yi tasiri a zuciyoyin makarantan mu.

Wanne abu ne ya fi ɗaure miki kai a harkar rubutu?

Yadda wasu daga cikin marubutan ke ɗaukar kai da zafi, ko ganin idan ka samu wata nasara ka fi ƙarfin ka kula wata. Da kuma yadda wasu marubutan ke da saurin ɗaukar zafi a kan wata maganar da za su ji an ce akan wance, ba tare da sun bincika sun tabbatar wancen nan haka ta ce ba ko saɓanin hakan, don duk wanda zai ɓata wani a wurinka, tabbas kai ma yana kai taka maganar wurin wani.

Da wanne lokaci ki ka fi jin daɗin yin rubutu? Kuma wanne yanayi ne ya fi kawo miki sauƙin ilhamar rubutu?

E, to! Ni ina rubutu a kowanne lokaci da ma kowanne yanayi, muddin ina da lokaci, ko da kuwa wurin da mutane, idan har ba magana za su mini ba to, suna harkarsu ni ma zan iya rubutuna. Don haka safe, rana, ko dare muddin ina da lokaci ba ni da abin yi to, zan iya yin rubutuna. Sau da yawa a mafarki na kan samu wani jigon labarin, ko kuma ina aiki ko tafiya to, ina samun natsuwar samun jigo, da yadda ma ya kamata na gina labari na kaina.

Kin taɓa fuskantar matsalar satar fasaha?

A’a, gaskiya sai dai ko a samu sunan labari ya zo ɗaya.

Yaya dangantakar ki take da masu bibiyar littattafanki?

Akwai zumunci mai ƙarfi a tsakanimu gaskiya, ta yadda har suke iya ziyarta ta, ko kirana a waya mu yi zuminci.

Shin ban da rubutu wacce sana’a ko aiki ki ke yi?

Ina sayar da littafaina, ina sayar da magunguna na GHT, ina kuma sayar da kayan yara na gwanjo masu kyau.

Wasu marubutan adabi suna komawa rubutun fim, shin ke ma kina da ra’ayin komawa?

E, in sha Allahu. Ina koyon rubutun fim, kuma ina fatan a nan kusa kaɗan zan fara rubuta labarin fim, da yardar mai duka.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Guntun gatarinka, ya fi sari ka ba ni.

By ukarofi