
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗaya daga cikin sanannun malaman addinin Musulunci a Nijeriya kuma jagoran Ɗarikar Tijjaniya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya rasu bayan shafe shekaru 100 a duniya.
Rahotanni sun bayyana cewa, fitaccen malamin ya rasu ne a daren Laraba wayewar Alhamis, lamarin da ya kawo ƙarshen jagorancinsa na miliyoyin al’umma a Nijeriya da ma ƙasashen waje.
A ranar 28 ga watan Junin 1927 aka haifi shehin malamin a Garin Nafaɗa da ke da tsohuwar jihar Bauchi, wanda a yanzu kuma yake cikin Jihar Gombe.
Ya sadaukar da tsawon zangon rayuwarsa wajen karantarwa musamman Al-ƙur’ani, jagorancin ɓangarorin addini da ayyukan jinƙai.
A cewar wani daga cikin iyalansa, za a sanar da lokacin jana’izarsa nan ba jimawa ba.
