
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan na ɗaya daga cikin ɗaruruwan masu sanya ido daga ƙasashen waje na zaɓe a ƙasar is Guinea Bissau, wanda a yanzu haka ya karɓe mulki da sojoji suka yi ya rutsa da shi.
Hakan na zuwa ne sa’o’i kaɗan gabanin sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar a hukumance.
Hakan na nufin Jonathan da sauran baƙi masu sanya ido akan zaɓen da aka gudanar ba za su iya barin ƙasar ba domin sojoji sun rufe iyakokin ƙasar baki ɗaya, tare da dakatar da zaɓen gaba ɗaya.
Al’amarin ya samo asali ne bayan da manyan ƴan takara biyu, wato hamɓararren Shugaban ƙasar, Umaro Sissoco Embalo da Fernando Dias sun yi iƙirarin samun nasara a zaɓen.
Kazalika, dakarun sojojin sun kuma sanar da dokar hana fita da kuma kama manyan jami’an da ke da alaƙa da zaɓen.
Jonathan ya je Guinea-Bissau ne a matsayin shugaban tawagar West African Elders Forum (WAEF) domin sanya ido akan zaɓen.
Sannan, ya ziyarci wasu rumfunan zaɓe a ƙasar kuma ya wallafa bayanai a kafafen sada zumunta kafin juyin mulkin.
Mutanen da ke tare da shi sun ce yana cikin ƙoshin lafiya, amma ba shi da damar barin ƙasar sakamakon sabon sauyin jagorancin ƙasar.
Har’ilayau, sojojin suna kuma ƙoƙarin katse sashen Intanet, lamarin da ya sa ake samun tangarɗa wajen sadarwa a ƙasar.
Hakan ya sa ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suka fara nuna damuwa kan tsaron manyan ’yan siyasa da jami’an zaɓe.
A cikin wata sanarwa, Jonathan da wasu shugabannin Afirka sun yi alla-wadai da juyin mulkin duba da yadda ya zama barazana ga tsarin dimukraɗiyyar ƙasar.
