Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
Wasu matasa a kasuwar Shuwarin ta Jihar Jigawa yankin Ƙaramar Hukumar Kiyawa sun afka wa wani jami’in tsaro da sara da gatari da wasu muggan makamai a masayar dabbobi ta Shuwarin a daidai lokacin da wasu mutane su ka yi masa ihun ɓarawo.
An ce waɗannan mutane da ake zargin ɓarayin ne sune suka yi masa ihun ɓarawo domin su kuɓutar da ɗan uwansu, shine mutane da ba su sani ba suka afka masa da suka sakamakon harbi da bindiga da shi wancan jami’in tsaro ya yi a kasuwar.
Duba da wani yanayi na rashin tsaro da ake fama da shi a Arewacin Nijeriya shine yas a jama’a suka afka wa jami’in tsaron da suka kasancewar ba ya sanye da kayan sarki har suka halaka shi.
Wani mutun da ya buƙaci asakaya sunansa a kasuwar ya ce, marigayin ya shiga karar dabobin ne a farin kaya ya kama wani mutum a masayar dabbobin da a kac e wai ƙasurgumin ɓarawo ne da hukuma take nema ruwa a jallo a yankin Jihar Bauchi.
Kama wanda ake zargin ya sa wani abokin tafiyarsa ya zagaya ta bayan wancan jami’in tsaro ya sheƙe shi da mari. Jin zafin marin ya sa ya saki ɓarawon da ya kama. Ganin haka sai ya ciro bindiga ya yi harbi sama. Yin harbinsa ke da wuya sai waɗanda ake zargin ɓarayin ne suka yi masa ihun ɓarawo, suna cewa ‘ɗan fashi jama’a’. Yin ihunsu ke da wuya shine mutane suka afka masa da duka da makamai har suka halaka shi.
Da yake ƙarin haske a kan lamarin, kakakin hukumar tsaro ta Civil Defense, Muhammad Badarudden, ya tabbatar da kisan jami’in tsaro mai suna Bashir Adamu Jibrin, ya ce, jami’in tsaro ne na ɓangaren binciken ƙwaƙwaf mai muƙamin sufiritanda.
Badarudden ya ƙara da cewar, waɗanda suka yi wa jami’in tsaro kisan gillar sun masa mummunan sara a kansa har sai da suka buɗe masa kansa da sara ta baya ƙwaƙwalwarsa a fili, kuma likitoci sun tabbatar da mutuwarsa.
Ya ci gaba da cewar, sun kama mutane uku daga cikin waɗanda ake zargin suna da hannu wajen halaka jami’in tsaron, yayin da su kuma waɗanda ya yi ƙoƙarin kamawar suka cika wandonsu da iska har zuwa yanzu ba a kama su ba.
Kamar yadda wasu mutane da na samu zantawa da su a kasuwar amma ba su amince a naɗi muryarsu ba su ka ce, bayan kashe jami’in tsaron, babu wanda ya san jami’in tsaro ne sai bayan da aka kashe shi a ka ga katin shaidar aikinsa da kuma wandonsa da ankwa, inda haka ne ya sa jama’a da dama masu hankali suka fara gudu daga kasuwar kafin jami’an tsaro su yi wa mayankar dabobin da masayar dabbobin ƙawanya.
A cewarsu, zuwan jami’an tsaro kasuwar ke da wuya suka shiga yi wa jama’a dukan ‘ya’yan kaɗanya, ba babba ba yaro, lamarin da ya sa mutane suka yi ta gudu suna barin dabbobinsu, wasu suna faɗuwa, inda jama’a da yawa suka ji rauni wasu kuma su ka yi targaɗe yayin da wasu ma suka karairaye. Wasu ɓatagari kuma suka yi amfani da wannan damar suka yi ta satar raguna da awakin jama’a suna tserewa da su.
Jami’in hulɗa da jama’a na Civil Defense, Malam Badarudden, ya ce, zuwa yanzu sun cafke mutane uku da suke zargin su da hannu dumu-dumu kuma za su samu bayanai akan waɗancan manyan ɓarayin da suke nema, waɗanda da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da su a gaban alƙali, domin su fuskanci hukunci.
