
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da gwamnatin Amurka ke ƙoƙarin tabbatar da kiyaye dokokin mallakar biza ga ɗalibai, ofishin kula da harkokin Amurka a Nijeriya ya gargaɗi ɗaliban Nijeriya da ke karatu a Amurka da su guji saɓa wa dokokin, inda yin hakan ka iya sa a ƙwace wa mutum biza da hana shi shiga ƙasar nan gaba.
A ranar Litinin ofishin ya bada gargaɗin ta shafinsa na X sakamakon matsi game da harkokin shige da fice a Birnin Washington akan ɗaliban ƙasashen waje musamman ƴan Nijeriya da sune suka fi yawa.
“Idan ka bar makaranta, ka ƙi zuwa aji or ka bar tsangayar da ka ke karatu ba tare da sanar da makarantarka ba, za a iya ƙwace bizarka ta ɗalibi, sannan za ka rasa cancanci bizar shiga Amurka nan gaba”, kamar yadda ofishin ya bayyana.
Ofishin ya kuma shawarci ɗaliban da su kasance masu kiyaye dokokin da mutunta kawunansu a matsayinsu na ɗalibai domin kauce wa fuskantar matsaloli yayin zamansu a ƙasar.
Jawabin ya biyo bayan samun yawaitar zama a ƙasar ga wasu sama da wa’adin bizarsu da damfara a harkar shige da fice, lamarin da ya sa hukumomin tsaron ƙasar suka hoɓɓasa wajen sanya ido ga ɗalibai a manyan makarantu gami da tabbatar da kiyaye dokokin bizar.
A ƴan shekarun nan gwamnatin Amurka ta tsaurara matakan kiyaye dokokin, lamarin da ya sa ta gudanar da sauye-sauye a harkokin tsaron cikin gida.
