Rashin Tsaro: ADC a Zamfara ta buƙaci Tinubu da Dauda su yi murabus

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), reshen Jihar Zamfara, ta yi kira ga Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da su yi murabus a matsayin gwamna da shugaban ƙasa idan har ba za su shawo kan matsalar rashin tsaro da ke addabar jihar ba.

Shugaban jam’iyyar na jiha, Kwamared Kabiru Garba Gusau ne ya bayyana hakan, a wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a yau Litinin, kan batutuwan da suka shafi ƙalubalen tsaro da durƙushewar tattalin arziki gaba ɗaya a jihar.

Ya ce wanzuwar duk wani buri na gwamnati shi ne tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa a ci gaban tattalin arziki da shugabanci na gari.

Ya koka da yadda ayyukan ‘yan bindiga suka sake kunno kai a Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yamma a matsayin wani mummunan bala’i, yana mai cewa dole ne gwamnati ta yi duk abin da ya kamata domin kare lafiyar fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba a yankin.

“Dole ne mu fadi gaskiya kuma jam’iyyar ADC ba za ta rungume hannun ta tana kallon mutanen Zamfara ana garkuwa da su, ana kai masu hare-hare da kwace musu dukiya daga wadannan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda ba tare da mun faɗawa gwamnati abin da za ta yi ba”.

“Ba mu ji daɗin rasa ‘yan uwanmu maza da mata a hannun ‘yan ta’adda ba, kuma jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyyar siyasa ta zo ceto jihar da ɗaukacin al’ummar ƙasar daga hannun shuwagabannin da suka Kasa ceton alummar su.”

A cewarsa, jam’iyyar ADC ce kaɗai aka kafa domin ceto jihar da ƙasa daga barazanar rugujewa.

Ya ce jam’iyyar ta karbi masu sauya sheka 75,000 daga jam’iyyun siyasa daban-daban na jihar.

A cewarsa, jam’iyyar ADC ta ga ya zama tilas ta samar da ƙarin katin zama mambobin jam’iyyar 100,000, domin tuni wasu ‘yan siyasa da dama suka bayyana sha’awarsu ta shiga jam’iyyar nan ba da daɗewa ba.

By ukarofi