
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da ƴaƴan ƙasa ke cigaba da ƙara wa Nijeriya kwarjini a idon duniya a ƴan kwanakin nan, ƴar shekara 17 mai suna Nafisa Abdullah Aminu daga Jihar Yobe, ta zama gwarzuwa a gasar ‘TeenEagle Global Finals’ a ɓangaren salon sarrafa harshen Turanci, wanda aka gudanar a Birnin Landon.
Rahotanni sun bayyana cewa, Nafisa, wadda ta wakilci Nijeriya daga makarantar ‘Nigerian Tulip International College’ (NTIC), ta doke sama da ɗalibai guda 20,000 daga ƙasashe 69 ciki har da waɗanda Turancin ne babban yarensu, lamarin ke ƙara fito da darajar ƴan Nijeriya a gida da waje.
TeenEagle gasa ce ta ƙasa-da-ƙasa da ake shirya wa ɗaliban sakandare daga ƙasashe masu amfani da Turanci da waɗanda ba su ba, domin jarraba ƙwarewarsu ta fuskar Turanci, zurfin basira da zalaƙar harshe.
A wata sanarwa daga Hassan Salifu, wanda shi ne babba a gidan su Nafisa, ya ce nasarar ta samu ne sakamakon jajircewa, horo da taimakon gwamnatin jihar Yobe ƙarƙashin Gwamna Mai Mala Buni wanda ya fuskanci harkar ilimi yadda ya dace.
Ya kuma jinjina wa ɗalibar bisa bajinta da ta yi wajen doke ɗaliban da aka mayar da Turanci babban yare a ƙasashensu, yana mai yabon jajircewarta da kyakkyawan kimtsi da ta yi wa al’amarin.
Nasarar da Nafisa ta samu ya sanya farin cikin a zukatan ƴan Nijeriya masu kishi a ciki da wajen ƙasa inda murnar hakan ya karaɗe shafukan sada zumunta.
Lamarin da ya sa ƴan Nijeriya da dama suke kira ga gwamnatin jihar da hukumomin tarayya da su karrama ta.
