
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya cire dakatarwar da ya yi wasu manyan jami’an gwamnati su guda 81 a jihar.
A sanarwar da Sakataren yaɗa labaransa, Monday Uzor ya fitar, gwamnan ya umarci kwamishinoni da manyan mataimaka da manyan sakatarori da aka dakatar da su a ranar 28 ga watan Yuli, 2025 da su koma bakin aikinsu nan da nan.
Daga cikin waɗanda dakatarwar ta shafa akwai Antoni Janar, kwamishinoni 25, manyan sakatarori 22, manyan mataimaka 14 da kuma mataimaka 24.
Rahotanni sun bayyana cewa hakan bai rasa nasaba da rashin halartar wani zama na musamman da gwamnati ta shirya da suka yi.
Lamarin da ya sa aka dakatar da su na tsawon wata guda ba tare da biyan albashi ba.
Haka kuma, a yayin haka ne gwamnan ya umurci jami’an da lamarin ya shafa da kada su sanya hannu a kowace takarda ta musamman na tsawon lokacin.
