Daga USMAN KAROFI
Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, ya bayyana damuwa matuƙa game da ci gaba da tashin hankali tsakanin ƙasashen Iran da Isra’ila, yana mai cewa rikicin na zama “wuta da ba wanda zai iya kashewa”. Guterres ya ce harin da Isra’ila ke kai wa Iran musamman a wuraren makamashi na nukiliya na iya janyo mummunar masifa a duniya.
A cewarsa, rikicin ya fara bazuwa zuwa wasu ƙasashe na yankin, inda aka samu hare-haren makamai daga ‘yan tawayen Houthi na Yemen zuwa Isra’ila da ƙasar Falasɗinu, sannan wasu ƙungiyoyin makamai a Iraq suna shirin tsoma baki. Guterres ya bayyana wannan a wata tattaunawa ta gaggawa da ya yi da kwamitin sulhu na MDD ranar Juma’a, inda ya roƙi a rage zafin rikicin domin kare makomar tsaron duniya.
Rahotanni sun nuna cewa sama da wurare 100 ne Isra’ila ta kai wa hari a Iran, ciki har da wuraren nukiliya kamar Natanz, Isfahan da Khondab. Hukumar lafiya ta Iran ta tabbatar da mutuwar fiye da fararen hula 224, yayin da fiye da mutane 2,500 suka jikkata. A gefe guda, Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai zuwa Isra’ila, inda birane kamar Tel Aviv, Haifa da Beersheba suka fuskanci hare-hare, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar Isra’ilawa 24 da jikkatar fiye da 900.
Guterres ya sake jaddada muhimmancin ba diflomasiyya dama, yana mai kira ga ɓangarorin biyu su dakatar da farmaki tare da bayar da haɗin kai ga hukumar makamashin nukiliya ta duniya (IAEA). Ya ce idan ba a shawo kan wannan rikici ba, zai iya rikiɗewa zuwa bala’in da zai shafi ƙasashe da dama a duniya baki ɗaya.
