Ba zan taɓa juya wa Yahaya Bello baya ba – Ododo

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya bayyana cikakken biyayyarsa ga tsohon gwamna Yahaya Bello, wanda ya ce shi ne ginshiƙin nasararsa a siyasa. Gwamnan ya ce Bello ya taka muhimmiyar rawa wajen cusa shi cikin tafarkin shugabanci, kuma har abada ba zai manta da irin wannan gata da ya samu daga gare shi ba.

Ododo ya yi wannan furuci ne bayan wata ziyarar ban girma da ya kai wa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, tare da sauran mambobin kwamitin zartarwa na jam’iyyar a Abuja. Ya bayyana Yahaya Bello a matsayin uba, yana mai cewa “kogi ba ta manta da asali ba”, sannan ya ƙara da cewa: “Na san daga ina Allah ya fito da ni, kuma na san wanda Allah ya yi amfani da shi.”

A cewarsa, ko da ace Yahaya Bello ya fusata da shi, ya kamata mutane su ɗauke shi a matsayin rikici tsakanin uba da ɗa, ba cin amanar siyasa ba. Gwamnan ya ce: “Idan kuka ji uban gidana dina ya fusata da ni, don Allah ku roƙa mini gafara a wajensa, amma ni ba zan taɓa cin amanarsa ba, kuma ba zan taɓa bijire masa ba.”

By ukarofi