Gwamnatin Tarayya za ta samar da cibiyar na’urorin bin diddigi don bunƙasa tsaro a ruwa da ci-gaban tattali

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Muhammad Matawalle MON ya sanar da samar da Cibiyar Na’urorin Bin diddigi ta ƙasa-da-ƙasa reshen Yammacin Afirka wanda Hukumar Yankunan Ruwa ta Ƙasa za ta jaogranta.

Matawalle ya faɗi haka ne a taron Ranar Yankunan Ruwa ta Duniya ta 2025 da aka yi a Abuja.

Ya ce, za a yi hakan ne da nufin inganta ayyuka ya yankunan da ƙarfafa alaƙa a tsakanin ƙasashen da ke shiyyar domin ciyar da ɓangaren gaba.

Ya kuma ce, Gwamnatin Tarayya tana aiki tuƙuru wajen ganin ta inganta tsaro a tashoshin ruwan Nijeriya da kulawa da albarkatunta.

Haka kuma, sabuwar cibiyar za ta sanya Nijeriya ta zama kan gaba wajen amfani da ababen ci-gaba na zamani da jagorancin harkar gaɓar ruwa a yammacin Afirka da ma sama da haka.

Ministan ya bayyana cewa, cibiyar za ta taimaka wajen bunƙasa harkokin tattalin arziƙi ta hanyar faɗaɗa ayyukan tashoshin jiragen ruwa da makamantansu.

By Babaji