
Daga BELLO A. BABAJI
A yayin gudanar da wani ɓangare harkokin shugabancinsa a Farisa, Shugaba Bola Tinubu ya gana da Babban Mai bai wa Shugaba Donald Trump Shawara kan harkokin Afirka, Massad Boulos.
Boulos, siriki ne ga Trump sakamakon ɗansa, Michael Boulos na auren ƴar Trump, wato Tiffany.
A wata sanarwa ta kafar X, Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya ce an gudanar da tattaunawar ne a ranar Alhamis, inda aka taɓo batutuwa da suka shafi tsaro na shiyyoyi da ya mayar da hankali kan samar da zaman lafiya a gabashin ƙasar jamhuriyar dimokuraɗiyyar Kwango da kuma haɗin kan tattalin arziƙi a sassan Afirka.
Ya kuma ce, tattaunawar ta nuna yadda gwamnatin Shugaba Tinubu ke aiki haiƙan musamman kan harkokin difulomasiyya da ke tsakanin Nijeriya da Amurka.
Sun kuma tattauna yadda za a faɗaɗa damammakin haɗin kan tattali a Nahiyar Afirka.
Hakan ya a samu ne sakamakon ƙoƙarin Nijeriya wajen zama fage na zuba jari a Afrika ta hanyar inganta masana’antu da samar da ayyukan yi gami da samar da ci-gaban ababen more rayuwa a Nahiyar.
