Ribas: Mata sun yi zanga-zangar neman dawo da Gwamna Fubara a Fatakwal

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a ne aka samu dandazon mata akan titin Aba dake Fatakwal, Babban Birnin Jihar Ribas, inda suka gudanar da zanga-zangar neman dawo da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Udo mulkin jihar.

An fara zanga-zangar ne a babbar hanyar inda suka yi tattaki zuwa gidan Gwamantin jihar riƙe da alluna da ke nuna rubutun ‘Bring Back Fubara’, Save Our Democracy’ da sauran su.

Matan, waɗanda galibinsu iyaye ne da matan aure, sun yi magiya ga Shugaba Bola Tinubu da ya ɗage dakatar da gwamnan da wasu zaɓaɓɓu domin dawo da harkokin jagorancin demokraɗiyya a jihar.

Wasu daga cikin ƴan zanga-zangar sun koka game da rikicin siyasa da aka yi fama da shi a jihar, inda suka ce duk da haka, gwamnan ya na iya bakin ƙoƙarinsa na sauke nauyin da aka ɗora masa.

Sun kuma ce, sun yi zanga-zangar ne da nufin kare martabar demokraɗiyya ba don cimma wata manufa ta siyasa ba.

Ganin yadda rikicin siyasar jihar ya yi ƙamari ya sa Shugaba Tinubu ya dakatar da zaɓaɓɓun jami’an gwamnatin jihar da ɗora jagora na wucin-gadi, wato ‘Sole Administrator’ a watan Maris, 2025.

By Babaji