Gwamnatin Tarayya ta sanya haramcin shekaru 10 ga waɗanda suka wuce wa’adin bizarsu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Tarayya ta shirya hukunci mai tsanani ga waɗanda wa’adin bizarsu ta haura watanni shida da ƙarewa, inda ta ce akwai haramta shiga na shekaru biyar, yayin da kuma zai zama na shekaru goma ga waɗanda nasu ya ƙare da shekara ɗaya.

Haka kuma mutum zai biya tarar dala 15 ga kowane kwana ɗaya da ya ƙaru akan ƙarewar wa’adin. Za a fara hukuncin ne daga ranar 1 ga watan Agusta.

Ministan Harkokin Cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya faɗi hakan a Legas yayin ganawa da masu-ruwa-da-tsaki a ranar Juma’a, a lokacin ƙaddamar da sabon tsarin gudanar da bizar.

Ga bayanin wasu daga cikin gyare-gyaren bizar da aka yi kamar yadda jaridar ‘News Point Nigeria’ ta ruwaito: “…the automated Landing and Exit Cards, Electronic Visa, Expatriate Comprehensive Insurance, and an upgraded Combined Expatriate Resident Permit and Alien Card.”

Sauran sun haɗa da “..the Temporary Resident visa, Temporary Work Permit, and revised Expatriate Quota system.”

Ministan ya ce, an yi sabon tsarin ne don toshe kafar amfani da bizar da wa’adinta ya ƙare a tsakanin al’umma da kuma tattara bayanai na daidai daga masu amfani da ita.

Ya kuma ce, daga cikin abinda sabon tsarin ya ƙunsa shine sabonta katin kafin wa’adinsa ya cika da kuma tabbatar da bin sa yadda ya kamata acikin al’umma.

By Babaji