An kashe jagoran ƴan bindiga, Gwaska da wasu gommai a Katsina

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Dakarun sojoji a Katsina sun yi nasarar kashe jagoran ƴan bindiga, Gwaska da wasu da adadinsu ya kai sama da 100 a ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta’addanci a Arewa maso Yammacin jihar.

Kwamishinan Harkokin Cikin gida da Tsaro na jihar, Dakta Nasiru Mu’azu ya bayyana hakan a wata sanarwa, ranar Juma’a.

Ya ce, lamarin ya auku ne a yayin da ɓangarorin tsaro suka ƙaddamar da salon ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar da ma Shiyyar Arewa maso Yammacin Nijeriya.

A yayin atisayen ne dakarun suka ƙwato dangogi biyu masu jigida da ɗaiɗaita su da kuma wasu muggan makamai.

Ya bayyana cewa sojojin Birget ta 17 da jami’an sojojin sama na atisayen ‘213 Forward Operating Base’ suka ƙaddamar da harin akan ƴan bindigar a ranar 10 ga watan Afrilu, a yankunan Mununu Bakai, Zango, Jeka Arera Malali da Ruwan Godiya a Ƙananan Hukumomin Ƙanƙara da Faskari.

A yayin haka ne suka kashe Gwaska, wanda mataimaki ne ga ɗaya daga cikin jagororin mayaƙan ISWAP, bayan ya sauya sheƙa daga Ƙaramar Hukumar Ɗan-Musa zuwa Dajin Munumu.

Haka kuma, dakarun sun kai hari a yankin Dutsen Wori dake Garin Ɗandume ta iyakar Ƙananan Hukumomin Faskari da Sabuwa, inda nan ma sun kashe ƴan bindiga da dama.

By Babaji