Hukumar Yaƙi da Masu Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya, NDLEA, ta kama wani fasinja a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport, da ke Abuja bayan da aka gano yana da alamun hodar iblis a cikinsa.
A wata sanarwa da kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar yau Lahadi, ya ce mutumin, Paul Okwuy Mbadugha, mai shekar 54, wanda ɗan kasuwa ne da zai tafi ɓietnam, ya shiga hannun hukumar ne a ranar Litinin 12 ga watan Agustan nan na 2024, yayin da yake shirin hawa jirgin ƙatar Airways zuwa ɓietnam, bayan yada zango a Doha.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Bayan kwana huɗu da aka sanya shi yana bahaya, Mbadugha ya kasayar da ƙullin hodar ibilis 88 da nauyinsu ya kai kilogram 1.171.
Hukumar ta ce, a bahasin da mutumin ya bayar ya ce, shi ɗan kasuwa ne a Legas kuma wani abokinsa ne a Isolo, ya ba shi ƙullin ya haɗiye domin kai wa ɓietnam a kan kuɗi dala 2,000.
Haka kuma hukumar ta NDLEA ta ce jami’ant sun kama wani babban kulli na na ganyen wiwi da nauyinsa ya kai kilogram 800, da aka ɓoye a kwalayen taliyar yara, da nufin kaiwa ƙasar Kongo.
Hukumar ta ƙara da cewa, bayan da aka bi diddigin inda kayan ya fito an kama wani mutum mai suna Nnamani Sunday Sunny a kasuwar Alaba International market, a yankin ƙaramar hukumar Ojo a Legas.
