Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Da hantsi Binta (ba sunanta na asali ba ne) mai shekaru talatin da biyar, na kwance a rumfar da ke tsakar gidanta, tana shan iska, sakamakon tsananin zafin ranar da ake fama da shi, sai barci ya ɗauke ta, saboda sauro ya hana ta runtsawa cikin daren jiya. Ashe ba ta san daga wannan barcin ba za ta sake farkawa ba, sai a ƙiyama.
Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji’un! Na san mai karatu zai so jin ƙarashen abin da ya faru, wanda kuwa amsar na da nasaba da kanun sharhin da nake so in yi ne a wannan makon. Abin da ya faru kuwa shi ne, a lokacin da Binta ke kwance tana barci a cikin gidanta, bayan ta rufe ƙofar gidan saboda kada wani ya yi mata shigowar bazata, ashe Yusuf ɗan yayarta da suke unguwa ɗaya, wanda shekarunsa bai wuce goma sha bakwai ba, ya hauro katanga ta cikin lungun gidan. Da shigowar sa kuwa sai ya lallaɓa ya ɗauki taɓaryar dake bakin ƙofar kicin a jingine, ya runtuma mata a ka, nan take ta mutu ko shurawa ba ta yi ba. Shi kuwa sai ya ɗauki wayarta da ke yashe a gefen ta ya fita cikin hanzari, ya buɗe ƙofar gidan ya tafi wajen abokinsa, don ya raka shi wajen da zai sayar da wayar.
Bayan da labarin rasuwar Binta ya karaɗe unguwa, har mahaifiyar Yusuf da take ‘yar uwa a wajen Binta ta samu labari, ba ta yi zaton ɗanta ne ya yi sanadiyyar aikawa da ƙanwarta lahira ba. Sai bayan da bincike ya tashi, sannan abokin Yusuf da ya raka shi sayar da wayar ya je wajen baban abokin nasa ya bayyana masa cewa ɗansa ne yayi wannan kisan gilla, saboda ya sace wayar gwaggonsa. A lokacin da yake ba da wannan labarin tuni Yusuf ya tsallake ya bar gari zuwa ƙauyen mahaifinsa, da sunan zai yi musu kwana biyu kafin ya dawo. A ƙarshe dai Yusuf ya shiga hannun hukuma, kuma yana can yana fuskantar hukuncin da kotu ta yanke masa, daidai da shekarunsa.
Wannan labari da mai karatu ya karanta ba na ƙirƙira ba ne, tabbas ya faru da gaske, sai dai canjin suna da na yi. Dalilina na fara buɗe wannan rubutu nawa da labarin kisan gillar da aka yi wa Binta a cikin gidanta, shi ne domin in nuna mana irin tsananin da wannan mummunan harka ta satar waya ta kai. Ta tashi daga laluben aljihu, zuwa barazana da makami don a karɓi waya, har ta kai ana tsallaka katanga a shiga gidan mutum a kashe shi don a ɗauki wayarsa.
Wata marubuciya Maryam Muhammad Sani ta rubuta a shafinta na Facebook, saboda razana da tashin hankali da ta ji game da lamarin, “Wannan masifa ta ƙwacen waya Allah Ya yi mana maganin ta. Lamarin ya wuce na karɓa a hanya, har ya kai ga a ɓalla shago ko a haura gida a karɓa. Allah mun tuba! Allah Ka yafe mana Ka rufa mana asiri…”
A daidai lokacin da nake wannan rubutu wata kafa a manhajar Facebook ta wallafa labarin aika-aikar da aka yi wa wata mai suna Safiya Saminu Bawa a Birnin Kano, wacce masu ƙwacen waya suka datse mata hannu a Unguwar Sheka. Haka ma a makon da ya gabata wasu masu ƙwacen waya a garin Gombe suka daɓawa wani magidanci wuƙa ya mutu har lahira, sannan suka ta fi da wayarsa.
Kashe mutane da jikkata wasu da dama da ɓarayin waya ke yi na cigaba da zama musiba kuma babban abin tashin hankali, musamman a jihohin Arewa, irin su Kano, Kaduna, Gombe da Jos. Hukumar Kula da ƙididdiga ta ƙasa (NBS), ta fitar da wani rahoto da ke bayyana cewa, tsakanin watan Maris na shekarar 2023 zuwa watan Afrilu na 2024, an sace wa ’yan Nijeriya wayoyin sadarwa da yawansu ya zarce Miliyan 26. Wannan adadi ba ƙaramin abin damuwa ba ne, duba da halin matsalar rashin tsaro, da matsin tattalin arziƙi da ake fuskanta a arewacin ƙasar nan. Wani abin ɗaga hankali da waɗanda aka sace wa waya suke fuskanta shi ne yadda ake samun wasu da ke amfani da layukan wayoyin mutane da ake sacewa suna cutar masu layukan wayoyin suna kwashe musu kuɗaɗen su daga asusun su na banki ko amfani da lambobin wasu mutane da ke cikin wayar, domin yi musu kutse a nasu lambobin wayar.
Kamar yadda muka sani, wayoyin sadarwa a yanzu sun sauya daga matsayin na’urar sadarwa ko kiran waya kawai ba, ta zama na’urar adana bayanai, na’urar cinikayya da musanyen kuɗaɗe, na’urar karatu da adana littattafai, da ɗaukar hotuna da bidiyo, har ma da ɗauka da watsa labarai. Satar waya, na nufin satar bayanai, satar dukiya, katsewar kasuwanci, katsewar karatu, da shiga cikin matsalar tsaro. Haka kuma ɓatagari masu kutse cikin giza-gizan sadarwa suna amfani da bayanan sirri da mutane ke adanawa a wayoyinsu wajen yi musu sakiyar da ba ruwa.
Matsalar satar waya ba akan farar hula kaɗai ta tsaya ba, har ma da jami’an tsaro. Wasu rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewa, a cikin wannan watan kaɗai wasu masu satar waya sun kashe wasu sojojin Nijeriya biyu, Laftanar IM Abubakar a Unguwar Sarki, da Laftanar Kwamanda M. Buba, a Unguwar Kawo. Wannan ya haɗa har da manya da ƙananan jami’an gwamnati da masu faɗa a ji a cikin al’umma. Kamar a Jihar Kano, an kashe wani malamin addinin Musulunci, Alaramma Jabir Lawan Abdullahi, a kusa da Gidan Sarki, cikin watan da ya gabata na Mayu.
Lallai akwai buƙatar jami’an tsaro su tashi tsaye wajen shawo kan wannan babbar matsala ta tsaro da ke neman gurbin zama a cikin jerin matsalolin da suke addabar ƙasar nan. Kodayake, bayanai na nuni da cewa, jami’an tsaro na ‘yan sanda na ƙoƙari wajen zaƙulo inda ake kai wayoyin da ake sacewa. An gano cewa, kashi 90 cikin ɗari na waɗanda ke kai rahoton sace musu waya wajen ’yan sanda, da ƙyar kashi 11.7 cikin ɗari suke samun a gano musu wayoyinsu. Sai dai yadda mutane ke zargin ’yan sanda suna karɓar kuɗaɗe a wajensu kafin a binciko musu wayoyinsu da aka sace, yana kashe gwiwar mutane dake tunanin zuwa kai koke wajen ’yan sanda, wasu ma sun gwammace su bar wa Allah.
Marubuciya Maryam Muhammad Sani cikin rubutun da ta yi a Facebook, ta bayyana yadda suka yi da wani matashi da ke ce mata shi ma ya sa a ƙera masa irin wuƙar da masu ƙwacen waya suke amfani da ita, don ya kare kansa. Kodayake, ta nuna rashin dacewa kan mutane su mallaki wuƙaƙe don kare kansu, amma ta ba da shawara da cewa.
Iyaye da ‘yan sanda (hukumomi) da shugabanni da al’umma dole sai mun haɗa kai bakiɗaya. Idan har ɗaya daga cikin waɗannan rukunan ya naɗe hannu, tabbas hakan zai haifar da naƙasu ga ƙoƙarin daƙile wannan matsalar. Allah Ya kiyashe mu mugun ji da mugun gani. Allah Ya raba mu da hau da dukkan abin ƙi.’
Lallai ya kamata gwamnati da jami’an tsaro, da ‘yan banga da ke ba da gudunmawa wajen kare al’umma su tashi tsaye su gano yaran da ke wannan aika-aika, don ɗaukar matakin doka a kansu. Yayin da a baya wannan matsala ta samu sauƙi a garin Jos, sakamakon haɗin kan da aka samu tsakanin jami’an tsaro da al’umma, amma yanzu wannan matsala tana sake kunno kai.
In kunne ya ji, jiki ya tsira.
