Yadda aka ajiye mu tare da kuraye da macizai – Janar Tsiga a hannun ƴan bindiga

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon Darakta-Janar na Hukumar Kula da ɗalibai masu yi wa Ƙasa Hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga, wanda ya shafe sama da watanni biyu a tsare, ya bayyana halin matsin da suka tsinci kawunansu a hannun ƴan bindiga.

Ya ce, da shi da sauran waɗanda aka yi garkuwa da su, an tsare su ne a wani jeji da ke kewaye da duwatsu da dabbobi masu haɗari.

Janar Tsiga, mai shekaru 72 ya bayyana cewa, daga cikin dabbobin da aka ajiye su de tare akwai kuraye da macizai da kunamu, inda har a wasu lokutan kurayen ke kewaye su da sunan suna neman abinci.

Ya kuma ce, a duk lokacin da sojoji suka kawo hari, sai ƴan bindigar su fito da su da nufin zama kariya ga farmakin sojojin, wanda cikin ikon Allah suka kawo i’yanzu a raye.

Ya ƙara da cewa, Mai bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan tsaro tsaro (NSA) da Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS) sun sha alwashin murƙushe ayyukan ɓata-gari.

Bugu da ƙari, ya ce har abin fashewa an jefo wa ƴan ta’addar, amma bai fashe ba, wanda hakan ya sa suka kawo shi kusa da inda ya ke kwance da nufin ya na taɓawa, abin ya tarwatse da shi, amma Allah bai sa hakan ya faru ba.

Har’ilayau, ya kuma yi godiya ga Malam Nuhu Ribaɗu (NSA) da Janar Christopher Musa (CDS) bisa ƙoƙarinsu, da miƙa shi tare da wasu 18 da aka ceto ga iyalansu, ranar Alhamis.

By Babaji