Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A daren ranar Juma’a ne babban limamin Masallacin Dutsen Tanshi, Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ya rasu.

Ɗaya daga cikin jami’an masallacin ya tabbatar hakan ta kafar Facebook.

Za a gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 10 na safiyar Juma’a.

A baya dai Malamin ya yi fama da wani rashin lafiya da ba a bayyana wa al’umma ba, musamman a cikin watan Ramadana, kana daga bisani ya rasu.

A makon da ya gabata ne ya dawo daga ƙasar Indiya bayan wata jinya.

Haka kuma bai samu damar gudanar da tafsirin azumin watan Ramadan ba kamar yadda aka saba a kowace shekara.

By Babaji