Sojojin gwamnatin ƙasar Myanmar sun ayyana tsagaita buɗe wuta na bai ɗaya, amma na wucin gadi a yaƙin basasar ƙasar, domin sauƙaƙa ayyukan ceto bayan girgizar ƙasar da ta afku a makon jiya, kamar yadda gidan talabijin ɗin ƙasar ya bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu a bala’in ya zarce 3,000.
MRTɓ ya ce, tsagaitawar za ta ci gaba ne daga ranar Laraba har zuwa ranar 22 ga Afrilu kuma da nufin samar da agajin jin kai cikin sauƙi. Sanarwar ta biyo bayan tsagaita wuta na wucin gadi na bai ɗaya da ƙungiyoyin gwagwarmaya masu adawa da mulkin soja suka sanar.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce, dole ne waɗannan ƙungiyoyin su guji kai hari a jihar, ko kuma su sake haɗuwa, in ba haka ba sojoji za su ɗauki matakan da suka dace.
Adadin waɗanda suka mutu sakamakon girgizar ƙasa a Myanmar ya kai 3,003, yayin da sama da 4,500 suka jikkata, kamar yadda gidan talabijin na MRTɓ ya ruwaito a yammacin ranar Laraba.
A maƙwabciyar ƙasar Thailand, adadin waɗanda suka mutu sakamakon girgizar ƙasar ya kai 22, tare da lalata ɗaruruwan gine-gine, yayin da mutane 72 suka ɓace.
A wani lamari da ke jaddada ƙalubalen kai agaji a daidai lokacin da ake yaƙin basasa a ƙasar Myanmar, rundunar sojin ƙasar ta ce dakarunta sun yi harbin gargaɗi bayan da ayarin motocin ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ƙasar Sin suka kasa ja da baya yayin da suke tafiya a yankin da ake fama da rikici.
Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta shaida wa kafofin yaɗa labarai cewa, tawagar ceto da kayayyakin da take da su na cikin koshin lafiya bayan afkuwar lamarin a ranar Talata.
Kakakin ma’aikatar Guo Jiakun, ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, Beijing na fatan “dukkan ɓangarorin na Myanmar za su ba da fifiko kan ayyukan agajin girgizar ƙasa, da tabbatar da tsaron ma’aikatan ceto da kayayyaki.
“Ya zama dole a kiyaye hanyoyin sufuri don ayyukan agaji a buɗe kuma ba tare da cikas ba,” inji Guo.
Kakakin gwamnatin sojan ƙasar Zaw Min Tun ya ce, ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ƙasar Sin ba ta sanar da hukumomi cewa, ana cikin wani rikici da ya ɓarke a daren ranar Talata, kuma tawagar jami’an tsaro ta yi harbi a iska bayan da ayarin motocin da suka haɗa da motocin gida suka kasa tsayawa.
Sojoji sun ƙoƙarta wajen tafiyar da ƙasar Myanmar bayan juyin mulkin da suka yi wa zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula ta Aung San Suu Kyi wadda ta lashe kyautar Nobel a shekarar 2021, abin da ya rage tattalin arziki da ayyukan yau da kullun, ciki har da kiwon lafiya, bayan yaƙin basasa.
Majalisar ɗinkin Duniya ta ce sama da mutane miliyan 28 a yankuna shida ne girgizar ƙasar ta shafa, ta kuma tanadi dalar Amurka miliyan 12 a cikin taimakon gaggawa na abinci, matsuguni, ruwa, tsaftar muhalli, tallafin lafiyar kwakwalwa da sauran ayyuka.
Yayin da fatan samun ƙarin waɗanda suka tsira ke ci gaba da dusashewa a ranar Laraba, masu aikin ceto sun zaƙulo wasu mutane biyu da ransu daga rugujewar otal a babban birnin Myanmar, Naypyidaw, da na uku daga wani masaukin baƙi a wani birni – kwanaki biyar bayan girgizar ƙasar mai karfin awo 7.7, amma yawancin ƙungiyoyin sun sami gawarwaki kawai.
