Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta samu nasarar damƙe wani magidanci mai suna Suleiman Mamuda ɗan kimanin shekaru 30 ɗan asalin garin Bayawa da ke ƙaramar hukumar Augie yayin da yake kan hanyarsa ta tserewa bayan ya kashe matarsa mai suna Umaima Maidawa.
Bayanin da wakilin Blueprint Manhaja ya tattara sun nuna cewa kisan ya biyo bayan barazanar da Umaima ke yi masa ne na cewa ita fa yanzu ta gaji da zama da shi saboda ba shi da kuɗi kamar yadda ya ke a baya saboda haka tana so ta kashe auren don ta auri ɗaya daga cikin mutanen da suka neme ta da aure a baya wanda ya yi sanadiyyar har ta yi yaji, bayan da aka mayar da ita ɗakin ta da kwana ɗaya tana kwance a ɗakin ta tana bacci sai ya nemo ƙotar kwasa ya buge ta a ka, inda nan take ta mutu shi kuma ya ɗauke jinjirin su da ba a bayyana shekarun sa ba ya kama hanya ya gudu.
Bayan da bayanin ya fito sai aka shelanta a gari. Sai dai an yi nasarar kama shi a wani gari da ake kira Katami da ke jihar Sokoto.
Majiyoyi da dama sun labartawa wakilin Blueprint Manhaja da cewa Suleiman Mamuda ya sha yi mata (Umaima) barazanar shi ne zai zama ajalin ta idan ba ta shiga taitayin ta ba.
Wata mai kama da wannan a unguwar Sabon garin Kanta da ke garin Argungu wani matashi mai suna Ibrahim dan shekaru 16 ya soke yayan sa Yusha’u Attahiru ɗan shekara 31 da wuka har lahira sanadiyyar ya hana shi faɗa da wani mutum.
Malam Attahiru mahaifinsu ya bayyana cewa ko da abin ya faru ba ya gida, a lokacin da ya zo ya je babbar asibitin Argungu inda aka ajiye gawar ya yi addu’a samun rahama ga mamacin kuma ya ce ya yafewa wanda ya yi kisan tare da addu’ar Allah ya yafe masa shi ma.
Ya ƙara da cewa a matsayin sa na musulmi ya san wa’adin mamacin ya riga ya yi saboda haka ko ta wannan hanyar ko kuma wata a ranar sai ya mutu.
Haka-zalika bayan kwana ɗaya da faruwar wannan Ranar Alhamis kuma a kauyen Gidan Dabai da ke gundumar Bubuche da ke makotaka da garin Bayawa an sami rahoton karya wa wani Alhaji ɗan Ayya kafa da ya nemi lalata da matar Alhaji Garba Dan Chabu inda bayan shi kwarton ya yi ta baiwa matar kudi amma sai ta gayawa mijinta Alhaji Dan Ayya shi kuma sai ya umarce ta da ta karbi kudin a duk lokacin da ya ba ta, bayan wani lokaci ya bukaci su hadu a bayan gari bayan Sallar Magriba ita kuma ta nuna ba zai yiyu haka ba sai dai ya same ta a ɗakin ta.
Bayan ta gaya wa mijin ta Alhaji ɗan Ayya sai ya ce da ita ta sa lokacin da za su haɗu sai ya shirya da ‘yan uwan sa suka nemi waje suka ɓuya.
Shigar kwarton ke da wuya bayan ya cire kayan jikin sa ya kwanta kan gado sai suka yi wuf suka far masa da duka har suka karya masa ƙafa.
Majiyar jaridar Blueprint Manhaja ta nuna cewa yanzu haka yana wani gida a garin Argungu da ba a bayyana ba yana jinya.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi Sufurtanda Bashir Usman ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce yanzu haka yana nan sashen bincike kuma da zarar an kammala binciken za tura su zuwa kotu.
