Yadda ake zargin Sylva da tattara kuɗaɗen shirin hamɓarar da Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Sabbin takardun bincike na sirri da aka samu sun bayyana yadda ake zargin tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylva, da tattara kuɗaɗen da aka ce an yi amfani da su wajen ɗaukar nauyin shirin juyin mulkin da bai yi nasara ba kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bara.

Wani rahoton da jaridar PremiumTimes ta wallafa ya ce, rahoton ya samo asali ne daga dubban takardun bincike sama da 7,400 da hukumomin tsaro suka tattara domin gurfanar da waɗanda ake zargi da hannu a yunƙurin juyin mulkin. Wasu daga cikin waɗanda ake zargin na fuskantar shari’a a Kotun Soja da kuma Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Takardun sun haɗa da bayanan da waɗanda ake zargi suka bayar, bayanan asusun banki, saƙonnin sirri, rubuce-rubucen da ake zargin jagoran shirin ya ɓoye, da kuma rahotannin bincike.

A cewar rahoton, Sylva, wanda ya taɓa zama ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, ya haɗa kai da wasu abokansa wajen tara sama da Naira biliyan biyar da ake zargin an ware domin aiwatar da shirin.

Rahoton ya ce, kafin shirin ya rushe a watan Satumban 2025, Sylva ya ba da umarnin a fitar da Naira miliyan 785 domin gudanar da ayyukan da suka shafi shirin.

Ana zargin ya yi amfani da asusun kamfanin Purple Waves Limited, wani kamfanin gine-gine da harkokin filaye da ke Abuja, wajen isar da kuɗaɗen.

Daga nan ne aka ce kamfanin ya tura kuɗin zuwa wani mai sana’ar canjin kuɗi, wanda bisa umarnin Kanal Mohammed Ma’aji, wanda ake zargi da jagorantar shirin, ya rarraba kuɗin ga mutanen da aka ware wa ayyuka daban-daban.

Masu binciken sun yi zargin cewa kuɗin da suka shiga asusun Purple Waves sun fito ne daga manyan hanyoyi biyu.

Na farko, sun ce wani kaso ya fito daga kuɗin wata kwangila da Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) ta biya kamfanin.

Rahoton ya ce NDDC ta tura Naira biliyan 5.8 zuwa asusun kamfanin domin wani aikin kare gabar teku da kwato ƙasa, amma bai fayyace cikakkun bayanan kwangilar ba.

Na biyu kuma, ana zargin kuɗin sun fito ne daga rancen da SunTrust Bank da wani kamfani mai suna Yobygo Nigeria Limited suka bai wa Purple Waves.

An ce a watan Satumban 2025, SunTrust Bank ya bai wa kamfanin rancen Naira biliyan 2.9, sannan ya sake ba shi wani rancen Naira biliyan 1.2. Bayan haka, Yobygo Nigeria Limited ta ƙara tura Naira biliyan 1.07 zuwa asusun kamfanin.

Masu binciken sun ce wasu kadarori uku da aka yi amfani da su wajen samun rancen banki na da alaƙa da Sylva ko wani na kusa da shi.

Kadarorin sun haɗa da gidaje biyu da ke Thaba Tseka Street, Wuse II, Abuja da kuma wani fili a Guzape.

Rahoton ya ce darajar kadarorin ta kai kusan Naira biliyan 10.9.

An ce an fara rarraba kuɗin bayan asusun ya kai biliyan 5.2

Masu binciken sun ce lokacin da kuɗin da ke cikin asusun Purple Waves suka kai kusan Naira biliyan 5.2, Sylva ya bayar da umarnin a fara rarraba su.

Rahoton ya ce daga nan aka tura Naira miliyan 785 ta hannun kamfanonin canjin kuɗi zuwa ga Kanal Ma’aji domin gudanar da shirin.

Rahoton ya kuma yi zargin cewa domin tabbatar da canja wurin kuɗaɗen ya zama kamar na halal, an miƙa wa banki wasu takardun da ke nuna kamar ana biyan kuɗin wasu ƙananan kwangiloli da suka shafi babban aikin NDDC.

Sai dai wanda ya mallaki kamfanin canjin kuɗin ya musanta sanin waɗannan takardu.

Haka kuma jami’in kula da asusun a SunTrust Bank ya ce bai taɓa haɗuwa da masu sa hannu kan asusun Purple Waves ba duk da cewa bankin ya ba kamfanin rancen biliyoyin nairori.

Masu binciken sun taƙaita lamarin da cewa an yi amfani da halastattun kuɗaɗe wajen gudanar da haramtattun ayyuka. Rahoton ya ce, bayan kama Kanal Ma’aji a ranar 29 ga Satumban 2025, hukumomi sun gano har yanzu akwai kuɗaɗe masu yawa a cikin asusun da ake zargin suna da alaƙa da shirin.

Ya zuwa 20 ga Oktoban 2025, akwai Naira biliyan 4.3 a cikin asusun Purple Waves, yayin da wani asusun APG na kamfanin ke ɗauke da Naira biliyan 2.9.

Daga nan ne aka ba SunTrust Bank umarnin dakatar da duk wata mu’amala da asusun da ke ɗauke da Naira biliyan 4.3. Haka kuma an umarci mai sana’ar canjin kuɗin da ya mayar da Naira miliyan 306.6 da ba a rarraba ba zuwa asusun Rundunar ‘Yan Sandan Soja ta Hedikwatar Sojojin Nijeriya. Sai dai rahoton bai bayyana matakin da aka ɗauka kan asusun da ke ɗauke da Naira biliyan 2.9 ba.

A watan Oktoban bara, Timipre Sylva, wanda rahoton ya ce yana wajen Nijeriya, ya musanta hannu a yunƙurin juyin mulkin, yana mai cewa dukkan zarge-zargen jita-jita ne kawai.

A halin yanzu kuwa, wasu mutum biyar da ake zargin suna da alaƙa da shi na fuskantar shari’a a Abuja bisa zargin ɓoye inda yake.

By ukarofi

Leave a Reply