Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An kama mambobin ƙungiyar da ake zargin ‘yan tawayen Ambazonia ne a wani otel dake ƙaramar hukumar Takum ta jihar.
Dakarun Burged ta 6 na rundunar sojin Nijeriya dake shiyya 3, masu aikin wanzar da zaman lafiya mai taken “Operation Whirl Stroke, sun kama mambobi 4 na kungiyar ‘yan tawayen Ambazonia daga jamhuriyar a Kamaru a jihar Taraba.
An kama mambobin ƙungiyar da ake zargin ‘yan tawayen Ambazonia ne a wani otel dake ƙaramar hukumar Takum ta jihar.
Sakamakon samun sahihan bayanan sirri a ranar 18 ga watan Disamban da muke ciki, dakarun sun bi diddigi tare da damƙe mutanen.
A sanarwar da ya fitar, mai riƙon muƙamin muƙaddashin darakta kuma kakakin burged ta 6 ta rundunar sojin Nijeriya, Olubodunde Oni, yayin binciken farko yace, wadanda ake zargin sun yi iƙirarin cewar su wani bangare ne na ƙungiyar ‘yan tawayen dake da hannu a safarar makamai ta hanyar musayar ‘ya’yan coccoa da abokan hadin bakinsu dake Nijeriya.
An ƙwato wayoyin hannu guda 4 mutanen da ake zargin wadanda suke tsare a yayin da ake ci gaba da bincike.
