
Daga BELLO A. BABAJI
Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ce harin da sojojinta suka kai a Sakkwato ya nufi ƴan ta’adda ne a sansanin su wanda hakan ya kai ga kashe ƴan ƙauye.
Daraktan Labaranta, Manjo-Janar Edward Buba, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce harin ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 10.
Ya ce farmakin ya samu sansanin ƴan ta’addar ne inda daga nan ne ya tarwatse ya kuma shafi wasu mutane.
Ya bayyana cewa, gabannin kai harin a ranar 25 ga watan Disamba, yankin na fama da matsin lamba daga ƴan ta’adda, waɗanda suka samu maɓoya a kusa da ƙauyukan, kamar yadda wani bayanin sirri ya nuna.
Janar Buba ya ƙara da cewa an shirya kai farmaki ne kafin ranar 25 wanda jinkirin ya samu ne saboda ƙoƙarin tabbatar da ba a samu kuskure ba wajen ƙaddamarwa.
Kazalika ya bayyana cewa atisayen ya samu nazari na sirri don tabbatar da ayyukan ƴan ta’adda a yankin.
Har’ilayau ya ce jami’an sun yi nasarar kai farmakin tare da tarwatsa wajen da aka hara inda mazauna yankin sun tabbatar da cewa akwai mayaƙan Lakurawa a kusa da su.
