Yadda iskar gas ta CNG ta samu karɓuwa duk da ƙalubalen tashoshin sayarwa da tsada

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shirin amfani da iskar gas ta CNG da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar a matsayin madadin fetur ya fara samun karɓuwa a wurin ’yan Nijeriya, duk da cewa masu ruwa da tsaki na ci gaba da roƙon gwamnati ta magance matsalolin samuwar sa, ƙarancin ababen more rayuwa da kuma tsadar sauya injin mota zuwa inji mai amfani da CNG.

Wannan tsari na daga cikin muhimman sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɓullo da su a fannin makamashi, inda ake ƙoƙarin rage dogaro da fetur tare da bunƙasa amfani da ɗimbin arzikin iskar gas da ƙasar ke da shi.

Manufar ita ce rage tsadar sufuri, samar da ayyukan yi da kuma inganta muhalli ta hanyar rage hayaƙi mai gurɓata iska.

Domin hanzarta aiwatar da shirin, an ƙaddamar da Shirin Shugaban ƙasa kan CNG (PiCNG) a shekarar 2023, wanda ke da nufin faɗaɗa amfani da motocin da ke amfani da CNG musamman a harkar sufuri ta jama’a.

Wasu direbobi ’yan kabu-kabu sun bayyana cewa sun fara amfana da sauƙin farashin gas idan aka kwatanta da fetur. Sai dai sun ce har yanzu ba a ga gagarumin sauƙin kuɗin mota ga fasinjoji ba, saboda ƙarancin motocin da aka sauya zuwa CNG da kuma wahalar samun tashoshin sayen gas ɗin.

Wasu direbobi sun koka da tsawon layuka a tashoshin CNG, lamarin da ke sa su ɓata sa’o’i masu yawa a jira maimakon yin aiki. Hakan na rage musu yawan kuɗin shiga, musamman ga waɗanda suka karɓi motocinsu ta tsarin biya a hankali.

Baya ga matsalar tashoshi, tsadar sauya injin mota zuwa CNG na daga cikin manyan ƙalubale. Rahotanni sun nuna cewa farashin sauya mota mai silinda huɗu ya ninka cikin shekara guda, abin da masana suka danganta da tashin farashin dala. Wannan na sa direbobi masu ƙaramin ƙarfi ba sa iya cin gajiyar shirin duk da burinsu na yin hakan.

Masana makamashi sun bayyana cewa shirin CNG hanya ce mai kyau wajen samar da makamashi, domin bai dace ƙasa ta dogara da man fetur kaɗai ba. Sun kuma jaddada cewa CNG na da fa’idoji ga muhalli saboda yana fitar da ƙarancin hayaƙi mai guba.

Hukumar Kula da ƙera Motoci ta ƙasa (NADDC) ta tabbatar da cewa motocin CNG na da aminci muddin an yi amfani da ingantattun kayayyakin sauyawa da cibiyoyin da aka amince da su. Haka kuma, gwamnatin tarayya ta fara wasu shirye-shirye na tallafi, ciki har da rage farashin kayan sauyawa inji da kuma sauya motocin sufuri kyauta a wasu lokuta.

Jami’an shirin PiCNG sun ce yawan motocin da ke amfani da CNG ya ƙaru sosai idan aka kwatanta da shekarar 2023, tare da faɗaɗa cibiyoyin sauyawa da tashoshin cika gas a jihohi da dama. An kuma bayyana burin kai motocin da suka koma CNG zuwa miliyan ɗaya nan da shekarar 2027.

Duk da waɗannan nasarori, yawan amfani da fetur a cikin gida na ci gaba da ƙaruwa, alamar cewa sauyin zuwa CNG bai kai matakin da zai rage dogaro da PMS sosai ba. Wannan na nuna cewa akwai buƙatar ƙƙrin zuba jari a ababen more rayuwa, wayar da kai da kuma sauƙaaa farashin sauyawa domin shirin ya kai ga talakawan direbobi.

A ƙarshe, masu ruwa da tsaki sun amince cewa shirin CNG na da kyakkyawar manufa kuma ya fara nuna alamu masu kyau. Sai dai nasararsa za ta dogara ne kan yadda gwamnati da ɓangaren masu zaman kansu za su hanzarta samar da tashoshi, rage tsada da kuma tabbatar da cewa amfanin ya kai ga talakawan ’yan Nijeriya da ke fama da tsadar sufuri a kullum.

By ukarofi