Tinubu na gyara tattalin arziki domin kare dimukraɗiyyar Nijeriya – Dare

Spread the love

Daga MAHD MUSA MUHAMMAD

Mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwar jama’a, Sunday Dare, ya buƙaci ’yan Nijeriya su ba da goyon baya ga sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa ƙarƙashin ajandar “Renewed Hope”.

Dare ya bayyana haka ne yayin gabatar da lacca a taron jama’a da jaridar Daily Trust ta shirya a Abuja, inda ya ce lokacin da Tinubu ya karɓi mulki a shekarar 2023, Nijeriya na fuskantar hauhawar farashi, tangarɗar canjin kuɗi, tarin basussuka da kuma raunin kwarin gwiwar masu zuba jari.

A cewarsa, cire tallafin man fetur da kuma haɗa kan farashin canjin kuɗi sun zama wajibi domin gyara karkacewar tattalin arziki da kuma dawo da daidaito a tsarin mulki.

Ya bayyana cewa, matakan sun taimaka wajen kawo ƙarshen tsarin da ya janyo asarar kuɗin shiga tare da karkatar da anfani daga jama’a zuwa wasu ɓangarori marasa amfani.

Dare ya ƙara da cewa alamomi na baya-bayan nan sun nuna cewa ana fara samun murmurewa a tattalin arziki, inda ya ambaci ƙaruwar bunƙasar arziki, raguwar hauhawar farashi, karuwar ajiyar kudin waje da kuma kyautata gaskiya a harkokin kuɗaɗe na gwamnati. Ya jaddada cewa gyara ba saɓawa dimokuraɗiyya ba ne, illa wata hanya ce ta kare ta.

A cewarsa, cigaban Nijeriya zai ta’allaƙa ne da shugabanci mai jajircewa wajen gyara tsare-tsare da gina tsarin dimokuraɗiyya mai anfani ga kowa, ba wai ga wasu tsiraru kaɗai ba.

Dare ya bayyana jamhuriya ta huɗu a matsayin mafi tsawon lokacin da Nijeriya ta samu tana tafiyar da mulkin dimokuraɗiyya, duk da kalubalen da ke tattare da ita. Ya ce dimokuraɗiyya ba tafiya ce madaidaiciya ba, illa hanya ce ta koyo wadda take buƙatar gyara, sake dubawa da daidaitawa da sauye-sauyen da ke faruwa.

Ya kuma lura cewa jinkirin da aka samu a bunƙasar dimokuraɗiyya a Nijeriya ba wai saboda jama’a sun ƙi ta ba ne, sai dai saboda gazawar shugabanci da cibiyoyi wajen tafiyar da bambancin al’umma, samar da adalci da kuma gina halaccin siyasa ta hanyar daidaiton tattalin arziki.

A ƙarshe, Dare ya buƙaci ‘yan Nijeriya su haɗa kai wajen tallafawa sauye-sauyen da ake yi, yana mai cewa hazin kai na gaskiya yana samuwa ne ta hanyar yanke shawarwari masu anfani ga ƙasa, ba wai ta furuci kaɗai ba.

By ukarofi