Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS) ta sanar da tara kuɗin shiga da suka kai Naira tiriliyan 7.28 a shekarar 2025, wani ci gaba da aka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin tattalin arziki da hukumar ta taɓa samu cikin ‘yan shekarun nan.
Babban Kwanturola Janar na Hukumar Kwastom, Bashir Adeniyi, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin bikin Ranar Kwastom ta Duniya ta 2026, inda ya jaddada cewa sauye-sauyen da aka aiwatar a tsarin aiki, amfani da fasaha ta zamani da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki ne suka haifar da wannan nasara.
A cewarsa, kuɗin da aka tara sun zarce burin da aka sa wa hukumar na shekarar da ya kai naira tiriliyan 6.5, inda aka samu ƙarin kusan Naira biliyan 697 sama da abin da aka yi hasashe, wato fiye da kashi 10 cikin 100.
Adeniyi ya bayyana cewa wannan nasara ba wai kawai ta nuna ƙarfin tattalin arzikin hukumar ba ce, har ma tana nuni da cewa gyare-gyaren da aka shigo da su na fara haifar da sakamako mai ma’ana.
Ya kuma ƙara da cewa, idan aka kwatanta da shekarar 2024, inda aka tara naira tiriliyan 6.1, kuɗaɗen shigar na 2025 sun ƙaru da kusan naira tiriliyan 1.18, wanda ke nuna ƙarin kusan kashi 19 cikin 100 cikin shekara guda.
Shugaban hukumar ya jaddada cewa wannan ƙaruwar ba ta samo asali ne daga tsauraran matakai da ke takura halastattun ‘yan kasuwa ba, sai dai daga inganta bin doka, amfani da bayanai yadda ya kamata, fasahohin dijital da kuma tsaftataccen tsarin sa ido.
A cewarsa, hukumar ta samu daidaita manufarta ta tara kuɗaɗen shiga tare da sauƙaƙa harkokin kasuwanci, musamman a ƙarƙashin yarjejeniyoyin kasuwanci na yankuna da na duniya.
“Wannan nasara ta zo ne sakamakon ingantaccen tsari da haɗin kai da bangaren masu zaman kansu, ba tare da tauye haƙƙin halastattun masu shigo da kaya da masana’antu ba,” inji shi.
Hukumar Kwastom na daga cikin manyan hukumomin gwamnati masu samar da kuɗaɗen shiga ba tare da dogaro da man fetur ba, inda take da alhakin sauƙaƙa kasuwanci, tara haraji, tsaron kan iyakoki da kuma daƙile fasa-ƙwauri.
Masana tattalin arziki na ganin cewa wannan ci gaba na iya taimakawa gwamnati wajen rage matsin lambar bashin cikin gida, tare da ƙara ƙarfin aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa.
