Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da shirin fitar da sabuwar ƙa’ida da za ta sauƙaƙa samar da katinan cire kuɗi tare da inganta yadda na’urorin ATM ke aiki a faɗin ƙasar.
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ne ya bayyana hakan ta bakin mai ba shi shawara na musamman, Fatai Karim, a wani taro da aka gudanar a ƙarshen mako.
Ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin da bankin ke yi na magance matsalolin samun kuɗi a hannu da kuma dawo da amincewar jama’a ga tsarin biyan kuɗi ta na’urorin zamani.
A cewar CBN, sabuwar manufar za ta tilasta bankuna su daidaita yawan katinan cire kuɗi da suke fitarwa da kuma adadin na’urorin ATM da suke da su. Ana sa ran hakan zai taimaka wajen rage dogayen layuka a gaban ATM, yawan lalacewar na’urori, da kuma matsalar rashin kuɗi a wasu wurare.
Cardoso ya jaddada cewa yawan gazawar ATM da ƙarancin kuɗi a na’urori na ci gaba da kassara amincewar jama’a ga tsarin biyan kuɗi na zamani, duk da ƙaruwar mu’amalar kuɗi ta hanyar lantarki a cikin tsarin banki.
Ya ce, “Ba da jimawa ba, Babban Bankin Nijeriya zai fito da wata sabuwar ƙa’ida domin gyarawa da inganta halin da ake ciki, musamman dangane da yadda bankuna ke fitar da katina idan aka kwatanta da adadin ATM da suke da su.”
Masana harkar kuɗi na ganin cewa wannan mataki na iya kawo sauyi mai ma’ana idan aka aiwatar da shi yadda ya kamata, domin zai tilasta bankuna kara zuba jari a kayayyakin more rayuwa na ATM maimakon mayar da hankali kawai kan yawan katinan da ake rabawa kwastomomi.
A shekarun baya-bayan nan, ’yan Nijeriya sun sha ƙorafi kan wahalar cire kuɗi ta ATM, lamarin da ya sa da dama ke komawa amfani da tsabar kuɗi ko kuma biyan kuɗi ta hanyoyin da ba na hukuma ba. CBN na fatan sabbin matakan za su taimaka wajen daidaita tsarin tare da ƙara ƙarfafa amincewa da harkokin kuɗi na zamani a ƙasar.
