Manoma 74,000 za su fara noman kanunfari a faɗin Nijeriya – Kungiyar Masu Noman Kanunfari

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Masu Noma, Sarrafawa da Tallan Kanunfari a Nujeriya ta sanar da shirin fara noman wannan amfanin gona karo na farko a tarihin ƙasar nan, inda ake sa ran manoma sama da 74,000 za su shiga aikin a lokacin daminar shekarar 2026.

Babban Mai Tsara Ayyukan ƙungiyar, Abdullahi Shuaibu, ne ya bayyana hakan a ƙarshen wani taron horas da masu neman a yankin Arewa maso Yamma, wanda aka gudanar a Cibiyar Binciken Noma ta IAR da ke Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

Ya bayyana cewa, shirin zai haɗa aƙalla manoma 2,000 daga kowace jiha cikin jihohi 36 na Nijeriya da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.

A cewarsa, wannan mataki zai zama babbar hanya ta bunƙasa noma mai daraja da kuma faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga daga ƙasashen waje.

Shuaibu ya ce, kanunfari tsiro ne na yankunan zafi wanda zai iya bunƙasa a sassa da dama na Nijeriya, yana mai ƙarawa da cewa kowane manomi da ya shiga shirin gwajin zai samu ingantattun iri da sauran kayan noma domin noma rabin hekta na gona.

Ya jaddada cewa buƙatar kanunfari na ƙara ƙaruwa a kasuwannin cikin gida da na ƙetare, musamman daga kamfanonin abinci da na magunguna. A cewarsa, idan shirin ya tabbata, Nijeriya za ta zama ƙasa ta biyu a Afirka bayan Zanzibar ta Tanzaniya wajen noman kanunfari a matakin kasuwanci.

A nata ɓangaren, Maijidda Abdulkadir, Ma’ajiya ta ƙungiyar reshen Jihar Kaduna, ta bayyana cewa jiharta wadda ta shahara wajen noman citta za ta rungumi wannan sabon shiri hannu bibbiyu. Ta ce manufar ita ce rage talauci, samar da ayyukan yi da kuma bai wa mata manoma dama ta musamman.

Ta kuma tabbatar da cewa an riga an samo ingantattun irin kanunfari daga Tanzaniya domin tabbatar da nasarar shirin, tare da kira ga gwamnatocin jihohi su ba da cikakken goyon baya.

Wani mai ba da shawara kan harkokin kuɗi ga ƙungiyar, Aminu-Yahaya Masanawa, ya bayyana cewa noman kanunfari na iya samar da riba fiye da yawancin hatsi da kayan lambu. Ya ce hakan zai taimaka wa manoma su kauce wa asarar da suke fuskanta sakamakon faɗuwar farashin amfanin gona a kasuwa.

Farfesa Mukhtar Abdullah na cibiyar IAR, ABU Zariya, ya ƙaddamar da littafin koyarwa kan yadda ake noman kanunfari, wanda ke ɗauke da cikakken bayani daga yadda ake shuka shi har zuwa hanyoyin kasuwanci da dabarun duniya.

Masana sun ce shirin na da fa’ida mai yawa ga tattalin arzikin karkara, samar da ayyukan yi ga matasa da mata, tare da buɗe sabuwar hanya ta samun kuɗaɗen shiga ga Nijeriya daga fitar da kaya ƙasashen waje.

By ukarofi