Yadda jadawalin gasar Europa ya kasance

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An kammala zagayen ’yan 16 na gasar Europa, inda a yanzu ƙungiyoyi 8 suka samu damar tsallakawa zagayen daf da na kusa da na ƙarshe a gasar.

Manchester United da Sevilla za su kara a wasan quarter final a gasar zakarun Turai ta Europa League.

Ƙungiyoyin da suka kai wannan mataki sun haɗa da Sporting Lisbon da Feyenoord da Juventus da Manchester United da Roma da Sevilla da Union Saint-Gilloise sai kuma Bayer Leverkusen.

Arsenal da aka saran za ta taɓuka abin azo a gani a gasar ta bana, ganin irin tagomashin da ta ke samu wajen jagorantar gasar Frimiyar Ingila, Sporting Lisbon ta fidda ita daga gasar a bugun daga kai sai me tsaron gida.

A ranar Juma’a ne aka haɗa yadda ƙungiyoyin za su haɗu a matakin daf da na ku sa da na ƙarshe da kuma zagayen kusa da na ƙarshen na gasar.

A ranar 13 ga watan gobe ne kuma za a yi karawa tafarko na zagayen, sannan a buga karawa ta biyu a ranar 20 duk dai a watan na goben.

Jadawalin wasannin na a Europa:

  • Manchester United da Sevilla
  • Juventus da Sporting
  • Feyenoord Rotterdam da Roma
  • Bayer Leverkusen da Royale Union Saint Gilloise

Wasannin farko a quarter finas:

Ranar 13 ga watan Afirilun 2023;

  • Manchester United da Sevilla
  • Juventus da Sporting
  • Feyenoord Rotterdam da Roma
  • Bayer Leverkusen da Royale Union Saint Gilloise.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *