Yadda kaso 59 ya zama na yara daga ɓatattun ƴan Nijeriya 23,659 – Rahoto

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kimanin ƴan Nijeriya guda 23,659 suka ɓata da har yanzu ba a same su, lamarin da ya jefa iyalai 13,595 cikin ƙunci, kamar yadda rahoton kwamitin ƙasa-da-ƙasa na tallafi (ICRC) ya bayyana.

Jami’in ICRC, Benson Lee ya fitar da rahoton a Yola, kamar yadda rahotanni suka bayyana inda yayin jimamin ranar tunawa da mutanen da suka ɓata da tallafa wa iyalansu.

Lee ya bayyana cewa, yawan ɓatar mutane a Nijeriya na da alaƙa mai ƙarfi da yawan rikici tsakanin al’umma a matsanancin rashin tsaro a shiyyar Arewa-maso-Gabashin Nijeriya.

Ya ce, kaso 67 na al’amarin da suka samu rahoto a kai ya samo asali ne daga Jihar Borno sakamakon ayyukan ta da ƙayar-baya na ƙungiyar Boko Haram.

Ya kuma yi ƙamari ne yayin suka gano cewa kaso 59 na mutanen yara ne marasa galihu, lamarin da ya nuna yadda rikici ke tasiri akan yara da marasa galihu.

Jami’in ya ƙara da cewa, wahalhalunda iyalan suke fuskanta a sanadiyyar tattali, shari’a da ma tsarin zamantakewa duba da cewa da dama daga cikin ɓatattun su ke ɗaukar nauyin iyalansu.

By Babaji