‘Yan sanda sun kama wasu riƙaƙƙun ‘yan fashi da makami a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar ƴan sanda a Katsina sun kama wasu gungun yan fashi da makami da suka ƙware wajen ɓalle shaguna da ƙwacen wayar hannu a cikin garin Katsina.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar da sanarwar haka,ya ce dukkan su suna zaune a layin Ɗan Haƙo da ke unguwar shararrar pipe cikin garin Katsina.

A cewar sa sun haɗa da Abubakar Dayyabu ɗan shekara 19 da aka fi sani da Antu,sai Abdulrahaman Danjuma ɗan shekara 25 da ake kira Aguero da Dahiru Nuhu ɗan shekara 21 da ake kira Tsoho.

Sauran sun haɗa da Muhammad Yahaya ɗan shekara 21 da ake kira Lucas da Bello Balele ɗan shekara 34 da shima ake kira Na Ande.

Sai Abubakar Idris ɗan shekara 20 da ake kira Makale da Shafi’u Lawal Ɗan Fefe.

DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa ƴan sanda sun kama mutanen ne a maɓoyan su a shararrar pipe bayan samun labarin fasa babban shagon kayan masarufi a bayan babbar kasuwar Katsina.

Ya ce bincike da suka gudanar,an samu adduna guda biyu,wuƙaƙe guda biyu da dogon ƙarfe a maɓoyan su.

DSP Abubakar Sadiq ya ce da sauran ƴan sanda sun gama bincike za a gurfanar da mutanen a gaban kotu.

Kwamishinan yan sanda CP Bello Shehu ya tabbatar wa al’ummar jihar musamman a garin Katsina cewa rundunar za ta cigaba da tabbatar da kare rayukan al’umma da dukiyar su.

Ya nemi gudunmawar al’ummar jihar na bada bayanai na sirri kan maɓoyan miyagun mutane a jihar.

Ya kuma yaba da jami’an sa kan ƙwarewa da jajircewa da suke nunawa wajen gudanar da aikin su na samar da wanzuwar zaman lafiya.

By ukarofi