Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Mutane 5 ne aka tabbatar da mutuwarsu a ranar Talata a wani mummunar fashewar gas a kan titin Ojekunle, kusa da titin Ladipo, a unguwar Mushin da ke jihar Legas.
Kamar yadda rahotanni suka ruwaito, bam ɗin ya lalata motoci aƙalla 15, tare da lalata gidaje da dama a yankin.
Wurin da gobarar ta afku ya haɗa da makanikai, masu facin taya, dillalan iskar gas da sauran ’yan kasuwa.
Shaidun gani da ido da suka zanta da kamfanin dillancin labarai, sun ce, lamarin ya faru ne a kusa da wata Mama Emma, mai soyan ƙosai da misalin ƙarfe 7:30 na safe, yayin da wani dillalin iskar gas ke cika wani silindar gas ga abokin ciniki.
Shaidu suka ƙara da cewa, yayin da ake cike gas ɗin, abokin cinikin nasa ya samu kirar waya, wanda hakan ya haddasa gobarar.
Sodiq, abokin cinikinsa, Mama Emma da wasu mutane biyu sun ƙone ƙurmus, yayin da aka kwashe gawarwakinsu aka miƙa ga iyalansu domin yi musu jana’iza.
’Yan kasuwa da dama da lamarin ya faru a idonsu, sun bayyana mai sayar da iskar gas ɗin a matsayin mutum mai aiki tuƙuru da bai cancanci mutuwa ta irin wannan mummunar hanya ba.
Sama da motoci 15 da ke harabar wurin ne suka farfashe sakamakon gobarar.
Wasu daga cikin ɓaraguzan da bam ɗin ya haddasa na rumfanan da makanikai ke amfani da su sun tumbuƙe sun faɗo kan motocin da suka farfashe.
Wani makanikin da lamarin ya faru a gabansa mai suna Tajudeen Olorunwa ya shaida wa manema labarai cewa, motarsa ƙirar Toyota Highlander da ta wasu mutane huɗu da suka kawo gyara duk sun ƙone.
Olorunwa ya ce, bai taɓa samun irin wannan asara ba tsawon shekaru 24 da ya yi yana gyaran mota.